Ɗan adam baya taɓa dauwama cikin farin ciki ko baƙin ciki, yakan iya kasancewa cikin farin ciki a yau, gobe kuma ya tashi cikin baƙin ciki, ko kuma ya wayi gari cikin baƙin ciki daga baya kuma ya yammatu cikin farin ciki.
A lokacin da ƙunci ko damuwa suka tabbata ga ɗan adam musulmi, yana da hanyoyin da zaibi cikin sauƙi ya gusar da wannan damuwar dake addabarsa, misali kamar:
Sallah
Addu’a
Zikiri
Gaskiya
Haƙuri
Waɗannan basu bane kaɗai hanyar kawar da damuwa, amma sune mafiya shahara da kuma saurin mayewa mutum gurbin damuwarsa da farin ciki.
.