Hanyoyin da mace mai ciki zatabi domin zama cikin koshin lafiya da abinda ke Cikin cikinta

Hanyoyin da mace mai ciki zatabi domin zama cikin koshin lafiya da abinda ke Cikin cikinta

Idan mace tayi ciki yaron da yake cikinta yana zukan jininta sabida shine abincinsa wannan dalilin yasa mata masu ciki suna yawan samun karancin jini .

Yakamata ta samu nau’in abinci mai dauke da sinadarai masu gina jiki, kayan lambu, da kuma kayan mar-mari:

Wake
kifi
Nama
kwai da sauransu

Dakuma ganye da kayan itatuwa kamar su

Salat
kabeji
Alayyafu
zogole
Lemu
kankana
Apple dasauransu .

Wanda cin abinci lafiyayya yana karate’s mata jini , lafiya , yana karawa yaron da yake cikin ta lafiya da kaifin basira .

Rayuwar yau da kullum na mai ciki dole ya banbanta da na sauran mutane.

mace mai juna biyu bai kamata tadinga aikin wahala sosai ba, yakamata tadinga hutu ko wacce rana .

idan mace mai ciki bata da lafiya dole taje asibity domin gudun kada tayi amfani da maganin da zai zama mata matsala ,ko zai yakawo matsala ga yaron cikinta .

tsaftar muhalli da tsaftar jiki yana da amfani sosai ga mace mai juna domin kare kanta da yaron cikinta daga kamuwa da cututtuka .
d- maccen da take yawan amai yakamata tayi amfani da busheshshen abinchi wanda hakan zai rage yawan amai ko kuma ya tsayar da aman gabaki daya .

Zuwa awu (Antenatal) yana da amfani sosai wanda a lokacin awu za a auna aga yadda yaro ya kwanta a ciki da. kuma girmansa da kwanakin cikin.

Kuma ana auna aga wasu matsaloli masu kashe uwa da jaririnta domin a magance su, kamar su :

Hawan jini
Ciwon sugar na masu juna
Cutan kanjamau
Yawan Jini
Zazzabin cizon saura
Alamar Eclampsia
Ina gargadin mata da sudinga amfani da maganin karin jini da ake basu a wajen awu (Antenatal).

mafi yawan mata idan anbasu maganin karin jini mai makon suyi amfani dashi kullum, amma basa amfani da shi, da sunan basa son warin maganin , wanda wannan baya daya daga cikin dalilin da zaisa a hana mutum shan wannan maganin .

Asani dama chan magani ba Dan dadi ake shanta ba, illa Dan neman lafiya da neman kariya daga lafiya .

Sai Kuma daukan allurar tetanus, wannan wata allurace da akeyiwa mata lokocin awun ciki , amma mafi yawa mata basa son wannan allurar sabida rashin sanin amfaninta .

Gaskiya wannan allurar tanada amfani sosai wanda yana daga cikin amfaninta shine kare yaro daga kamuwa da wannan cutan nan mai hatsarin gaske wato ( tetanus ) .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *