HANYOYI MAFIYA SAUƘI DON RIBATAN RAMADAN

Ku daure ku karanta har ƙarshe, kuma kuyi ƙoƙarin ɗabbaƙawa, domin zai amfaneku da iyalanku. Sannan, ku tura ma wasu don suma su amfana (saboda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace: “Duk wanda ya nusar zuwa aikin alkhairi kamar wadda ya aikata ne”, ko kuma “yanada lada kwatankwacin ladan wanda ya aikata“.)

A wani hadisi, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace “… Ku ribaci abubuwa 7 kafin 7,” a ciki harda lokaci kafin rashinsa da lafiya kafin jinya. A duk lokacin da akace wani abu mai girma da matuƙar muhimmanci ga tarin albarka da ɗimbin lada yana tunƙarowa, toh dole sai an masa shiri na musamman, don ribatar sa yadda ya kamata. Kamar yadda muke tanadin kayan sallah da kuma abincin Ramadan, haka ya kamata muyi tanadi da shiri don amfani da lokutan mu a cikin watan azumi yadda ya kamata. Kamar yadda aka ruwaito Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana ƙara ɗamara ya tashi iyalansa a goman ƙarshe, toh ai mune ya kamata mu ƙara ɗamara, domin idan bamu saba aikin tun farko ba, toh idan goman ƙarshe sukazo ba zamu iya jurewa ba.

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama dai yace, “duk wanda Ramadan yazo ya fita baiyi abinda aka gafarta masa ba toh Aljannah ta haramta a gareshi”.
Ya ƴan’uwa masu albarka, kunga she abin sai mun dage sosai wajen ganin munyi shiri na musamman.

Mu haɗu a turmi na biyu, inda zamu fara bayani akan abubuwanda ya kamata mu fara ragewa ko barin yin su ko ƙaurace musu, tun kafin Ramadan ya shigo.

Allah Ya ƙara tsira da aminci ga fiyayyen halitta Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam da iyalansa tsarkaka da sahabbansa masu daraja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *