Yanda ake bandashen gurasa.
- Fulawa
- Yeast
- Gishiri,
- Mai
- Cabbage
- Cocumber
- Kuli
- Tumatir
- Albasa
Yanda Ake hadawa mataki na farko.
Da farko zaki tankade fulawarki kidan zuba gishiri kadan saiki dan kwaba yeas din da ruwan dumi saboda yayi saurin tashi bayan ya tashi saiki dakko nonstick dinki kidan shafa mai ki dora a wuta idan yayi zafi.
Sai ki dauko kwabin gurasarki kidinga fadada shi kina dorawa, idan kasan yayi ki juya ki maida saman haka zakiyi tayi harki gama bayan kin gama zaki yayyankata yanda kkeso.
Daman kin gama yanka kayan hadi kin soya mai kuma zaki fara zuba kuli kulin Wanda aka dakashi da Kayan hadi saiki dakko mai ki zuba.
Yadda Ake Gurasar Tanderu (Tukunyar Kasa).
A yau za mu koya yadda ake gurasar tanderu.
Gurasa abinci ne da ake yin sa daga fulawa, ya samo asali ne daga abincin Larabawa, gurasa abinci ne dake da matuƙar daɗi, da sauƙin sarrafawa da kuma dauƙan lokaci ba tare da ta yi komai ba.
Ana iya cin gurasa da abubuwa da ya samu, musamman ma gurasar tanderu ta fi daɗi, domin tanderu tukunya ce, wadda ake ginawa da ƙasa, kuma duk abin da aka yi shi a cikin tukunyar ƙasa ƙamshinsa daban yake.
Abubuwan Da Ake Buƙata:
- Fulawa
- Yis
- Kantu/ridi
- Sikari
- Gishiri
Yadda Ake HaÉ—awa
A sami fulawa a tankaɗe a zuba mata yis, sai a zuba ruwa a kwaɓa. Kada a kwaɓa ta yi ruwa, a kwaɓa ta da ɗan tauri.
Idan ana son Gurasa mai sikari, sai a zuba sikari a cikin kwaɓin; idan kuma mai gishiri ce, sai a zuba gishiri a cikin kwaɓin.
Idan lokacin zafi ne, za ta yi saurin tashi saboda dama yis zafi yake so; awa uku zuwa huÉ—u ya ishe shi ya tashi.
Amma idan lokacin sanyi ne yakan daɗe bai tashi ba. Idan ana so a yi gurasa da safe; to sai a kwaɓa fulawar tun da daddare.
Idan an tabbatar kwaɓin ya tashi, sai a zuba karare a cikin tanderu, a kunna wuta domin tanderun ya yi zafi.
Idan an tabbatar tanderun ya yi zafi sosai, kuma karan ya cinye sai a yayyafa ruwan kanwa a ciki.
A saka tsintsiya a share toka-tokar da ta maƙale a cikin tanderun.
Sai a kawo kwaɓin a cura shi ya yi faɗi, a faɗaɗa da hannu, yadda dai ake son fadinta ya kasance.
Idan kina son kantu/ridi sai a zuba É—an kaÉ—an a kan gurasar a tsakiya; idan kuma ba a so, shi kenan sai kawai a saka curin da aka yi a cikin tanderun.
Idan an gama sakawa, sai a kawo tire a rufe tanderun. Takan É—auki kamar minti ashirin zuwa ashirn da biyar kafin ta yi.
Ba ma sai an kalli agogo ba, da ta yi za a ji ƙamshi ya turare ko’ina a gidan.
Sai a kawo wuƙa da tire, a ringa saka wuƙa ana ɓamɓaro ta tana faɗawa kan tiren. Amma sai an yi a hankali saboda zafi, kada a ƙone domin tanderu yana da zafi sosai.