Hanyoyi 6 da za abi don kare jiki da fata a lokacin hunturu

Lokacin huturu lokacin ne da jiki da fatar mutane ke wahala matuka saboda kura da iskar da ake yawan fama da shi
Kamar yadda aka sani hunturu kan fara a tsakanin watannin Nuwamba zuwa Maris ne. Wannan lokaci fatar mutane kan rika yakunewa yana karkarcewa wasu ma har budewa yake.
Matsalolin da irin wannan canjin yanayin ke kawowa sun hada da bashewar leben baki, tsagewar kafafen hanci, mura, da dai sauran su.

Ga hanyoyin

A rika saka kaya masu nauyi kuma wadanda ke rufe jiki kaf da takalma da za su rufe kafafuwa domin kare mutum daga iska.
Za a iya shafa man kade domin shi man kade na da ingancin hana bushewar jiki
A rika shan ruwa a kowani lokaci ba sai an jira an ji kishi ba.
shafa mai a lebe da kafafen hanci domin kare su daga tsagewa
A rika yin wanka da ruwan dumi musamman da safe ko kuma da yamma
Za a iya cin abincin dake dauke da kitse, fiya, kifi domin suna dauke da sinadarin dake gyara fatar mutum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *