HAKKOKIN MIJINKI AKAN KI YAR’UWA

Hakkin miji abune me girman gaske, kisani miji ba abun wasa bane. Bayan ubangiji inda da akwai wanda za aima sujjada toh da macece za’a nemi taiwa mijinta

Wajibine ki girmama mahaifan mijinki, domin su suka haifa har kema kika samesa amatsayin miji ayau.

Wajibine ki girmamashi komi talaucinsa. Domin bashi ya za6i ya zauna haka ba ubangiji ne ya tsara masa. Haka karkiga yana da hakuri kice zakike fadamasa maganganu na raini da wulakanci ko yar wacece ke kuwa

Kar ganin yana da hakuri ko yaushe kike aikata masa kuskure da gangan abisa ganin ai inkikace ya hakura yana hakura… kisani duk randa kika kaisa bango zai dena hakurin zakuma ki dena jin dadinsa, bazaki kuma samun kanshi ba

Kada ki kuskura kisa aranki ko kuma wata Qawa ta fadamiki ki dauka cewa ba’a sirri da miji…. kul dinki baki da abokin sirri irin mijinki inde kika cire mahaifiyarki… inkuwa kikaqi to zaki qaraci nuqu-nuqunki kuma yana kallonki bazai nuna yasan me kike ba… tunda kin nuna kina da wayau ahaka zai barki…

Amma kiji tsoron randa zai amayar miki da abunda ke cikinsa daga ranar kuma daga lokacin kin koma tsoronsa kenan kuma kin nesa da farin ciki kenan

Banda kauracemasa a shimfida. Akwai matan da inba alkawari ko cin hancin wani abu mijinsu ya basu ba basa ta6a yadda dashi a shimfida saboda wulakanci irin nasu da rashin sanin menene auren ma… kisani ba wasa bane hakika akwai tsinuwar ubangiji akan dukkan matan dake kauracewa shimfidar miji… matukar neman da yake miki ba wanda Allah ya haramta bane

Wato kamar yadda wasu kan korafin miji na cewa saide a sadu ta dubura; ko saduwa alhalin mace na cikin jini… A irin wnn hali tabbas bazaki masa biyayya ba domin shima bai yiwa Allah da manzonsa biyayya ba. Kuma duk namijin dake haka tsinuwar Allah ta hau kansa koda kuwa matar kace ta sunnah kuma koda ka tursasata.

kada mace take bayar da izinin shiga gidansa ga wanda baya son shigarsu gidan. kamar wadanda ba yan uwa na jini ba, wadanda tasan komi wuya ba aure tsakanin su, koma wadanda ya nuna bayason shigarsu koda yan uwa na jinin ne, haka ma cikin kawayenki inyace baiso toh adena kurum

Haramun ne mace take ta yad’aa sirrin mijinta domin tozartashi

Ba abune me kyau ba ga mace takema mijinta barnar dukiya don ganin kurum yana da wadata. Kota rika daukar kayansa musamman na abinci ta rika kyauta dasu batare da izininsa ba…

Haramun ne dibar kayan miji kina sayarwa, musamman kayan abinci su shinkafa, dawa, masara da sauransu

Wajibinkine kula da yaransa da kuma ayyukansa na gida da suka shafesa, Haka yaran nan nasa koda kuwa wadanda bake kika haifa masa su bane.

Haramun ne ki cuci mijinki ta hanyar yiwa abokiyar zamanki sharri kisa ya saketa don kurum kina kishi da ita. Allah ya tsinema mai irin aikinki

Kada kike kausasa masa harshe, kina daga masa murya…. wato ya zamto kina fada masa magana mai zafi, tare da daga murya har wanda ke nesa koma amkota ace suna jiyowa koda kuwa ke ya zalunta. Hakan haramun ne a musulunci babu kyau….

Wajibine kike yin kokarin faranta masa rai. Sannan ki rika bashi uzuri akan wasu al’amuran koda kuwa kinfishi gaskiya.

Kada kiyi abinda zaisa shi yaji baya son zama dake a gida ko abunda zai sanya shi nisantar hira dake ko kaurace miki a shimfida.
Musamman yawan kawo masa bukatu, karancin tsafta da yawan korafi ko kawo masa hirar gidan wasu.

Haka wasu ruwayoyi sun kawo karin hakkokin miji kan matarsa kamar haka:

~ Yayin da wani sahabi ya bawa Manzon Allah (S.A.W) labari cewa: Yana da mata da idan ya kalle ta sai ta faranta masa rai, idan ya shiga gida da bakin ciki saita yaye masa shi, idan kuwa baya nan tana kare shimfidarsa bata ha’intarsa, kuma tana kare dukiyarsa da kula da tarbiyyar ‘ya’yansa.

Sai Manzon Rahama (S.A.W) ya bashi amsa da cewa: “Allah yana da ma’aikata, kuma wannan matar tana daga cikin masu aikin Allah, kuma tana da rabin ladan shahidai”.

Hakanan wata ruwaya ta nuna cewa: “Mace mai aiki a gidan miji daidai take da wanda yake Jihadi a tafarkin Allah”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *