Gwamna Kano Abba Kabir Ya Bayyana Dalilan Da Suka Janyo Aka Rushe Round Dake Gaban Gidan Gwamnati – Interestingasf

Dalilin da yasa aka rushe shatele-talen gidan Gwamnatin bayan shawarar kwararru da aka gano cewa, ginin baida inganci kuma ka iya rushewa tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024.

Cikin wata Sanarwa mai dauke dasa hannun Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, yace Ginin yayi tsawo da yawa da Hakan ka iya kawo cikas ga tsaron Gidan Gwamnati da kuma yawan cinkoso da ake samu.

Gwamnatin tace zata sake Gina wajen dan tafiya daidai da zamani domin ganin an kara taimakawa al’ummar jihar wurin ganin an kara samar musu da kayataccen birnin na jihar kano dama sauran ayyuka da zasu sabinta birnin na jihar nan bada jimawa cewar gwamnatin abba kabir yusuf.

Hakika jihar kano tana daya daga cikin manyan biranan kasar nigeria sannan itace land of marketing wannan dalilin yasa zamu kara mayarwa da hankali domin ganin an sabunta birnin na jihar nan bada jimawa ba inji sakataren gidan gwamnatin kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *