Gwamna Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje Yayi Martani Akan Sabon Gwamna Abba Gida Gida – Interestingasf

Zaɓabben Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf yayi kira ga al’ummar jihar Kano, musamman waɗanda suke gine-gine a filayen gwamnati, kama daga makarantu, wuraren addini dana al’adu, da asibitoci, maƙabartu da kuma gefen katangar Birnin Kano da su daina.

Abba kabir yusuf Zababben gwamnan yace yana shawartar mutane dasu daina, wadanda suka fara kuma su dakatar hakan domin matukar ya fara gudanar da aikin shi, zai tsaurara bincike sosai akan wannan badakala, da tsohuwar gwamnati jihar kano ta gudanar a mulkinta na jihar.

Wannan gargadin ya biyo bayan kudurin da yake dashi na dawo da tsarin birnin Kano, sakamakon ganin gwamnatin APC ta mayar da birnin na jihar kano koma baya a idon mutane dama jihohi da suka hada da Lagos, Kaduna Akwa Ibom, da sauran jihohi da dama na arewaci da kudancin kasar nan.

Yayin dashi kuma gwamna abdullahi umar ganduje yayi martani dangane da abinda sabon gwamna ya fada nacewa kada ya manta har yanzu dai shine gwamnan jihar kano don haka wannan kalaman da sabon gwamnan mai jiran gado yakeyi tamkar tayar da husuma ne cewar gwamna ganduje na jihar kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *