Gobara Tayi Sanadiyyar Kona Manyan Shaguna A Cikin Kasuwar Kurmi Dake Kano – Interestingasf

Wata gobara ta tashi a kasuwar kurmi dake cikin birnin jihar kano kamar yadda majiyar mu ta samu labari dangane da faruwar lamarin daga bakin wani bawan allah daya daga cikin wadanda abin ya faru dasu.

Gobarar data tashi anyi asarar dukiya mai tarin yawan gaske a cikin kasuwar ta kurmi dake cikin jihar kano, kasuwar ta kasance daya daga cikin manyan kasuwannin da ake matukar ji dasu a birnin kano.

Mutumin ya kara dacewa ba yanzu kadai aka taba irin wannan ba, a shekarun baya an tabayi saidai muce ubangiji allah ya kare mu, tare da iyalan mu da dukiyoyin da ‘ya’ya’yan mu da iyayen mu baki daya.

Hukumar kula da gobara ta jihar kano wacce akafi sani da suna Fire service, sun bayar da shawara dangane da jama’ar kasuwar cewa yakamata su rika kula da wutar lantarki tare dayin adu’a kowani lokaci domin neman kariya daga wurin allah.

Daya daga cikin manyan shahararrun ‘yan kasuwar yayi matukar godiya sosai dangane da wannan shawarar da suka samu daga wurin hukumar kula da gobarar ta jihar kano dabo dake nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *