Gaskiyar Abinda Yake Faruwa Tsakanin Baba Dan Audu Da Kuma Baba Rabe A Cikin Shirin Labarina

Wasu daga cikin masu kallon shirin labarina sunyi tsokani dangane da irin power da aka baiwa baba dan audu akan baba rabi’u wato baban sumayya na cikin shirin labarina dake zuwar muku a tashar saira movies kowace juma’a.

Kamar yadda wasu daga cikin ma’abota kallon shirin mai dogon zango na labarina suka bayyana cewa shirin labarina yana daya daga cikin shirin da al’ummar Arewa sukafi kallon shi aduk ranar juma’a akan YouTube.

Masu kallon shirin sun shaida mana cewa tabbas shirin yana matukar daukar hankali tare da darusa masu tarin yawan gaske saidai matsala daya da take faruwa a cikin shirin na labarina maganar gaskiya baba dan Audu anbashi power data wuce ka’ida.

Kamar yadda aka nuna a baya cewa tsakanin baba dan Audu da kuma baba Rabi’u sun kasance aminan juna wanda sanadiyyar neman kudi allah ya hadasu tare harta kasance suka zama aminan juna wanda dalilin haka suka hadu da Juma baban Hafsee.

Hakika baba rabi’u yayi matukar cin amanar Hafsee wanda a dalilin juna biyu da yayi mata har ta rasa ranta yayin da kuma ya nuna nadamar shi, daga baya wanda hakan ya janyo rigima tsakanin shi da Baba dan audu har yakawo Juma baban hafsee tare da ‘yan sanda cikin gidan baba rabi’u a cikin Labarina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *