Guji cin abinci mai yaji da wanda yake da maiko sosai saboda zai kara musu kishirwa sannan akwai zafin gari.
A ci abinci mai ruwa-ruwa, musamman ‘ya’yan itatuwa irin su ayaba, abarba, gwanda, da makamantansu.
A sha ruwan zafi kamar shayi ko koko ko kunu domin suna gyara ciki musamman bayan an dade ba a ci abinci ba.
A guji cika ciki fal da abinci – za ka ga wasu suna cin abinci sosai idan an sha ruwa.
Hakan yana da matsala. An fi so ka ci abinci kadan sannan ka huta yadda idan an jima za ka iya sake ci.
A guji shan taba da dangoginta saboda tana da illa.
Babu laifi idan an motsa jiki lokaci azumi – amma a yi shi saisa-saisa.