FALALAR ZIKIRI DA AMFANIN SA

Yawan zikri yana korar sheɗan
Yawan zikri yana jawo samun yardar Allah
Yawan zikri yana gusar da damuwa da baƙin ciki daga zuciya
Yawan zikiri yana jawo farin ciki da annushuwa da nasaɗi a zuciya
Yawan zikiri yana ƙarfafa zuciya da jiki.
Yawan zikiri yana haskaka fuska da zuciya
Yawan zikri yana jawo arziki
Yawan zikri yana jawo samun kwarjini da jin dadi da farin jini
Yawan yana jawo samun ƙaunar Allah ta’ala, samun ƙaunar Allah shine babban buri.
Yawan zikri yana jawo kusanci da Allah, har a wayi gari mutum ya samu matsayin ihsani.
Yawan zikri yana jawo komawa zuwa ga Allah ta’ala, cikin farin ciki
Yawan zikri yana buɗewa mutum kofa ta samun yarda, da kusanci (Alƙurbiyya) tsakanin sa da Allah ta’ala.
Yawan zikri yana buɗewa mai yinsa babun ilmi, duk sanda ya yawaita ambaton Allah, zai ƙara sanin Allah ta’ala.
Yawan zikri yana buɗewa mutum matsayin ganin buwayar Allah ta’ala, da isar sa.
Yawan zikri zai sa Allah ya ambaci mai yawan yi, duk sanda ya Ambani Allah, shima zai ambace shi.
Yawan zikri yana raya zuciya domin zikri ga zuciya kamar kifi ne a cikin ruwa, yaya kifi yake kasancewa idan aka raba shi da ruwa? Haka mutum zai kasance idan baya ambaton Allah ta’ala.
Yawan ambaton Allah yana zama kamar abinci ga zuciya da rai.
Yawan zikri yana washe zuciya ya goge tsatsa daga cikin zuciya.
Yawan zikri yana kankare zunubi
Yawan zikri yana kare mutum daga ɗimuwa da gafala.
Yawan zikri idan yana tuna Allah a cikin yalwa da wadata , Allah zai fidda shi daga cikin halin tsanani.
Yawan zikri yana tsaratarwa daga saukar azaba.
Yawan zikri yana jawo saukar nutsuwa da saukar rahma, da lulluɓewar Mala’iku,
Yawan zikri yana shagaltar da harshe ga barin giba da gulma da ƙarya Annamimanci, da ashariya.
Majalisin da ake zikri, sheɗan baya zama a wajan
Albarka tana sauka a Majalisin da ake zikiri.
Yin zikri yana kare mutum daga hasarar lokaci, da tashi da warin mushen jaki daga majalisi.
Duk wanda ya ambaci Allah a ɓoye, har ya yi hawaye don ganin girman Allah, zai shiga inuwar al’arshi ranar Alƙiyama.
Idan yawan zikri ya ɗaukewa mutum hankali, har ya zama baya rokon wata bukata, Allah zai bashi fiye da dukkan masu roƙo suka roƙa.
Zikri shine mafi saukin ibada mara wahala kuma ga yawan lada.
Daga cikin falalar zikiri, yana jawo a dasawa mutum bishiya a gidan Aljanna, kamar yadda yazo a hadisi, Duk wanda ya ce Subhanallahil azeem wa bihamdihi.
Daga cikin falalar zikri, Kalmomi guda biyu masu saukin faɗa akan harshe masu nauyi akan sikeli, abin ƙauna a wajan Allah, Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil azeem.
Dawwama a cikin zikiri yana ƙare mutum daga taɓewa.
Zikri yana zama a kowane hali, babu sharaɗin sai da Alwala ko tsarki.
Yawan zikri haske ne, a duniya da ƙabari da makoma da siraɗi.
Yawan ambaton Allah shine tushen komai, idan ka sami arziƙin yawan sa ka gama sumun dukkan komai daga Allah.
Zikri yana kusanta abinda yake nesa, na buƙatu kuma yana nisanta abinda yake kusa, na damuwa da baƙin ciki.
Zikri yana tashin zuciya daga baccin gafala.
Yawan zikri yana jawo samun ɗanɗano mai faranta rai.
Mai yawan ambaton Allah, kada ka damu domin Allah yana tare da kai.
Yawan zikri yayi daidai da fita yaƙi da ciwar da dukiya mai yawa.
Ambaton Allah shine tushen nuna godiya ga Allah, domin duk wanda baya zikri baya godiya.
Zikri yana jawo samun ni’ima daga Allah kuma yana tunkuɗe Sakar fushin Allah. Mafi darajar mutane a wajan Allah shine wanda harshen sa ya zamo ɗanye a wajan ambaton Allah ta’ala.
Allah ta’ala da Mala’ikun sa suna yin salati ga mai yawan ambaton Allah.

  1. Yin zikri shine Asalin samun soyayyar Allah da tsira daga faɗawa cikin maƙiya Allah ta’ala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *