“Ka yawaita yin karatun Alƙur’ani mai girma alhalin kana mai azumi, ka taƙaita yin surutu, ka taƙaita kallace-kallacen fina-finai musamman ma a cikin wannan wata na ramadana mai albarka, ka mayar da hankalinka wajen raya azuminka ta hanyar ambaton Allah buwayi, domin haƙiƙa Allah zai ba wa azumi da Alƙur’ani damar yin ceto a ranar ƙiyamah, tsammaninka ka kasance daga cikin waɗanda za ka sami cetonsu a filin hisabi”
“Kada kayi wasa da damar da ka samu a cikin wannan watan mai albarka, ka ribaci kowace daƙiƙa ta hanyar daɗa neman kusanci da Allah ta’ala, kada ka biyewa son zuciya cikin abin da zai shagaltar dakai daga Allah”
“Ka ƙauracewa dukkanin aiyukan saɓon Allah, ka nufi ibadar Allah kaɗai a cikin wannan wata, karatun alkur’ani, kyauta, sadaqa, Kyautatawa, da dukkanin wasu kyawawan ɗabi’u nagari, sai Allah ya inganta azuminka”