DOMIN SAMUN LAUSHIN FUSKA DA MAGANCE KURAJE TARE DA HASKEN FATA

 1. zaki shanya bawon lemon zaki dana kwai sai ki daka suyi laushi ki kwaba da ruwa kirika shafawa kafin ki shiga wanka.

GYARAN FUSKA

 • tumatir
 • madara

ki kwaba madara da tumatir sai ki shafa tsawon minti talatin sai ki wanke.

 • garin alkama
 • zuma
 • madara

ki hada su ki rinka shafawa kafin ki shiga wanka.

 • lemon tsami
 • zuma

ki hadasu idan zaki kwanta ki rika shafawa idan zaki kwanta da safe ki wanke da ruwan dumi

 • man ridi
 • man kwakwa
 • man habba
 • miski

ki hada mayukan sai ki diga turaren miski ki rinka shafawa yana sanya fata tayi laushi da santsi.

MAN SHAFAWA DON LAUSHIN JIKI

 • man kwakwa
 • man kade
 • man angurya
 • man xaitun
 • almond oil
 • baby oil
 • madarar turare
 • cocoa buter

ki hada su duka ki rika shafawa jikinki xaiyi taushi sannan ki hada da sabulun.

 • sabulun xaitum
 • tetmasol
 • sabulun salo da gana
 • sabulun karas
 • sabulun cocumber
 • kurkur

ki hadasu ki rika wanka dashi amma sai anjure
ko ya kare ki siyo ki sake hadawa sannan ki rage shiga rana.

DOMIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

 • ruwan khal
 • zuma
 • man zaitun

zaki dora ruwan khal da man zaitun da zuma a wuta suyi zafi sai ki dan kara ruwa ki juya sosai ki wanke fuskarki sai ki nemi auduga ki rika goge fuskarki da hadin musamman wurin kurajen.

STEAMING NA FUSKA

 • kwai
 • zuma
 • nono

ki kwabasu sai ki shafa a fuska sai ki turara da ruwan zafi yakan hana fitowar kuraje tareda kashesu.

HASKEN FATA

1.zaki sami itacen sandal wood ki daka sai ki kwaba da kurkur da madara kike shafawa kafin kiyi wanka.

2.zaki kwaba kurkur da madara tare da kwaiduwar kwai kina shafawa kafin wanka safe da yamma.

GYARAN FUSKA

 • ruwan kal
 • mai zaitun
 • zuma

a sami ruwan kal cokali goma a zuba man zaitun cokali biyu, zuma cokali biyu, a dan dora a wuta yayi zafi sannan a kara ruwa kadan a kai a juya sosai sannan a sa auduga a dinga dangwala ana goge fuska da shi amma sai a wanke fuska da sabulu kafin a yi yana cire dattin fuska yasa fuska tayi kyau, ta yi fes.

STEAMING NA FUSKA

 • kindirmo (nono)
 • man zaitun
 • zuma

a hada a kwaba a shafa a fuska a sami ruwa mai zafi a ajeye a kasa, a kara fuska a kai,a lullube fuskar , zuma minti sha biyar ko goma, inda tiririn zai dinga dukan fuskarki in kin gama sai ki wanke fuskar.

ALAMOMIN MACE MEDAUKE DA SANYI

 1. Jin Zafi Lokacin Jima i
 2. Kaikayin Gaba
 3. Fitar farin ruwa agaba
 4. Gushewar Shaawa
 5. Warin Gaba

ALAMOMIN SANYI NA MAZA

 1. Kankancewar Gaba
 2. Saurin Inzali
 3. Kaikayin Matse matsi
 4. Kaikayin Gaba
 5. Gushewar Sha’awa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *