DOMIN MATA MASU CIWON MARA MUSAMMAN A LOKACIN AL’ADA

1- Asamu garin Girfa, garin Roman, garin shammar, garin Hulba, garin Babunaj, garin Bagaruwa. Kowanne chokali 1. Saiki dinga diban rabin chokali ko teaspoon kina dafawa ko kisa aruwan zafi, zakisha sau 2 safe da yamma bayan cin abinci.
2- Kisamu magaryar kura da tarauniya (kowanne dadai dadai, idan yakai cikin hannu to asa ruwa kamar kofi 5) da tsamiya kadan ko jar kanwa kidafa ki tace kidinga sha sau 2 safe da dare bayan cin abinci.
3- Kisamu zuma chokali 5, man Tafarnuwa chokali 2, saiki hadasu kidinga chan chokali 1 kafin kici abinci.
4- Kisamu garin kusdul hindi chokali 3, garin shazabu chokali 2, garin habbatussauda chokali 2, garin Babunaj chokali 2. Saiki dinga diban rabin chokali kina dafawa ko kisa aruwan zafi. Zakisha sau 2 arana.
5- Ki jiqa tsohuwar tsamiya dareda bushaeshshen gauta, idan yajiqu saiki dinga shan ruwan
6- Kisamu garin zaitun da garin habbatussauda kowanne chokali 2 ko 3 saiki dinga diban chokali 1 kina dafawa, kitace kisa zuma kisha safe da yamma.
7- Kisamu garin sassaqen marke da tazargade yawansu yazama daidai kamar 2 ko 3, saiki dinga diban chokali 1 kidafa da ruwa kofi 1, zakisa jar kanwa kadan. Zakisha rabin kofi sau 2 arana.
8- Kisamu ruwan zafi saiki dinga tsoma towel aciki ki tsantsane saiki dinga mannawa a mararki.
9- Kisamu citta da kurkum, da kananfari da mosoro da kimba kidinga yin shayi dasu
10- Shan ruwa mai yawa
11- Rage shan zaqi da abubuwan da suke qarawa jiki qarfi (caffeine)
12- Motsa jiki kadan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *