Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Kori Gwamnoni APC Daga Gidan shi Dake Adamawa

Wata majiya mai ƙarfi na kusa da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ta shaidawa News Point Nigeria a wata tattaunawa ta musamman ta wayar tarho cewa, gwamnonin sune kamar irin su:

Abdullahi Ganduje na Kano, Atiku Bagudu na Kebbi, Badaru Abubakar na Jigawa, Abdullahi Sule na Nasarawa da kuma tsohon shugaban tattalin arziki da kuɗi, Hukumar yaki da rashawa (EFCC) Nuhu Ribadu ya je rokon Atiku da ya amince da sakamakon zaɓe domin zaman lafiya da haɗin kai ga ƙasa.

Amma a cewar majiyar, Atiku yace ko shakka babu zai nemi ayi masa shari’a da dan takarar sannan kuma ya shaida musu ƙarara cewa baya son sake ganin kowa a cikin su a gidansa idan kuma suka kara ziyartar shi akwai hukunci mai tsauri da zai biyo baya atare dasu.

Ance Atiku abubakar ya fusata sosai, shiyasa yaƙi amince wa da ziyarar da suka kawo masa, an ce tawagar da ya gani ta Tinubu ta kara fusata shi, Majiyar ta ce Kamata ya yi Asiwaju ya tura wasu mutane daban ba su Ganduje ba wataƙila ya amince idan yaga Mutane ne da ba su da hannu a zaɓen ya yarda su tattauna.

An tabbatar da cewa, ya ji haushin daga cikin gwamnonin da suka ziyarce shi, haka kuma Atiku Abubakar ya yanke shawarar zuwa kotu kuma zai yi Shari’a da Tinubu har zuwa ƙarshen nasarar da zai samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *