Dalilin Satar Adaidaita Sahu Wasu Matasa Sun Hallaka Wani Matashi Aliyu A Garin Yobe Duba Kugani

Allah sarki wani matashi dan garin Gashua dake jihar Yobe ya rasa babur dinsa mai kafa uku jiya dalilin wasu Azzaluman matasa da suka ce ya kai su bayan gari da yamma ya fita dasu daga nan ba wani labari sai gawarsa da aka tsinta akan hanya anyi masa yankan rago sun tafi da babur din marigayin mai kafa uku.

Marigayin mai suna Aliyu wanda akeyiwa lakabi da (D) One matashi ne mai hazaƙa da neman na kansa, Maraya ne ba shi da uba shine yake faɗi tashi ya riƙe mahaifiyarsa tare da kannan shi maza da mata, Sannan kowa yayi masa kyakykyawar shaida a Unguwarsu.

Allah ya jikansa, ya gafarta masa Allah ya tona asirin wadanda suka yi masa wannan zaluncin, hakika wadannan matasan sun zalinci wannan bawan allah mai suna aliyu sun kashe shi a hanyar neman halak din shi ubangiji allah yayi masa rahama.

Yanzu haka dai rundunar jami’an tsaron ‘yan sandan jihar yobe dake garin Gashu’a sunyi alkawari tsaurara tsattsauran bincike dangane da wannan lamari daya faru na kisan wannan bawan allah mai suna aliyu D One dan asalin garin jihar yobe dake nigeria.

Jami’an tsaron sun shaida mana cewa hakika ba tun yanzu irin haka take faruwa ba, a garin musamman irin yankunan dake gefen garin anfi aikata irin wannan zalunci akan bayin allah masu fafutukar neman ganin sun rufawa kansu, asiri ta hanyar neman halak din su, cewar jami’an tsaron na jihar yobe state.

Saidai muce ubangiji allah ya kara tonawa wadannan mutane asiri hakika munyi alkawari kamowa wadannan mutane da suka aikata wannan zalunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *