Da yawa za ka ji macce tace tayi ta shan maganin Sanyi Amma ga banza.
Akwai wasu abubuwa da ya kamata a kiyaye lokacin da ake shan maganin Sanyi.
A LURA DA KYAU.
1- Idan Namiji da Matar sa suna dauke da wannan cutar , abinda ya dace dukkansu biyu zasu fara shan magani , bawai matar kadai ba , muddin daya daga cikinsu ne yake shan magani akwai matsala .
2- Duk matar da aka dora ta akan magani duk lokacin ta cire wandon ta yakamata ta wanke shi da antiseptic, kafin ta maido wannan shina yana taimakawa wajen warkewa .
3- Idan akaci gaba shan magani kuma ba’a kiyaye wasu hanyoyin da suke kawo wannan cutar ba shima akoi matsala sosai .Ma’anar haka shine dole ne a kaucewa hanyar da ka iya kawo cutar a jikin.
Misali dole ne ayi amfani da bayan gida mai tsabta.
A kiyaye wajen wanke dubura bayan an amfani da toilet.
4 Qauracewa Jima’i lokacin da ake shan magani yana taimakawa sosai wajen samun waraka.
Idan ba a kiyaye wannan ba gaskiya yana da wahala a samu waraka yanda ake bukata.
- Kar ki yi amfani da pants din wata komai lafiyar ta, kuma Kar ki ba ri wata tayi amfani da na ki pants.
- Ga matar da ke da kishiya dole ne su sha magani a lokaci daya kuma tare da mai gidan, idan ba ayi hka ko kin shanye maganin duniyar a banza.
Allah ya sa mu dace aamin.
PLEASE LIKE AND SHARE