GANYEN NA’A-NA-A
na’a-na’a wani ganye ne mai kamshi mai yado wanda ke son guri mai dausayi sai tayi yaduwa kafin wani dan lokacin duk guri ya cika na’a-na’a ganye ne mai matukar albarka yana da amfani sosai ga al’umma:
DAGA CIKIN AMFANIN GANYEN NA’A-NA-A
¹ shan ta nasa baki ya rinka kamshi koda yaushe sai yasa ake so wanda yaci wani abu mai sanya warin baki kamar albasa ko tafarnuwa ya sha na’a-na’a bakinsa zai daina warin.
amfani da ita na Hana fitowar kurajen fuska idan kuma ya Riga ya fito sai a dimanci shafa man za’a samu dacewa musamman ga masu maikon fuska.
yin hayaki da busasshe na’a-na’a Ayi turare da shi yana sanya kamshin jiki da kuma kanshi ga wurin da aka yi turaren haka kuma aka shaki kamshin da hayakin yana magani mura.
shafa danyen ganyen yana magani ciwon kai haka kuma idan Ana goge hakora da busasshe shi yana sanya hakora su yi haske.
matsala daukan ciki ga mata masu juna biyu kamar masu yin amai ko yawan zubda yawu in sun samu ciki sai su samu ganyen su wanke suna taunawa ko kuma su sanya a bakinsu don ya dauke musu yawan zubda yawu amma su guji amfani da shi idan sun haihu domin yana rage ruwan nono.
ga matan da suke fama da ciwon ciki na al’ada in sun ji cikinsu ya Fara ciwo sai su dafa ganyen suna sha.
GAME DA KARE KAI DAGA KAMUWA DA SANYI
idan har kana bin wannan hanya bakai ba kamuwa da cutar sanyi ba zai Kama mutum ba ta kowace hanya
idan ma ya Kama to za a rabu…..
yadda za a yi shine :
na farko idan Kai mai yawan shan shayi ne, duk lokacin da zaka sha shayin sai ka diga man tafarnuwa a ciki, ko kuma ka sami ruwan zaifi a kofi ka diga masa man tafarnuwa ka sha. ka rinka yin haka akai-akai kuma duk lokacin da zakayi wanka ka diga man tafarnuwa a cikin ruwa mai dumi sai Kayi wanka dashi zakayi mamaki