- Rashin Kula: Yawan lokacin da ka ba kowanne abu ke bayyana makomarsa. A misali, yawan lokacin da ka ke ba wa aikinka na bayyana yawan abinda zaka samu a karshe. Hakazalika soyayya kuwa, yawan lokacin da ka ba ta na nuna yadda za ta girma tare da habaka. Rashin kula kuwa na iya tarwatsa soyayyar namiji daga zuciyar mace.
- Rashin Yabo: Mata na son a nuna musu idan har abu ya birge ko kuma sun yi dai-dai. Mata na son a yaba kwalliyarsu, girkinsu, maganarsu da sauransu. Rashin yabo na sa soyayyar namiji ta fita daga zuciyar Mace.
- Kunci: Kunci na kawo rashin zaman lafiya a kowacce irin alaka. Ba soyayya kadai ba, hatta kawance babu mai son yi da mutum mai matukar kunci. Kunci na taka rawar gani wajen wargaza soyayyar namiji daga zuciyar Mace.
- Kalubalanta akai-akai: Mata basu kaunar namiji mai yawan kalubalantar su. Kalubalanta na fara shiga tsakanin masoya ake samun babbar matsala tsakaninta da masoyinta.
- Yi wa mace rikon sakainar kashi: Wasu mazan na soyayya da mace amma kiran mintoci kalilan na gagararsu. Wannan nuna halin ko in kula din na sa Mace ta daina son namiji kwata-kwata.
Akula dakyau mata sunada rauni kuma suna matukar son mai basu kulawa da wanda yadamu da damuwarsu.