Ana bukatar
- Curry
- Thyme
- Onga classic
- Citta
- Kanumfari
- Masoro
- Tafarnuwa
- Albasa
- Gishiri
Wannan sune main spices da kike bukatawajen suyar naman layya..inkina da bukata zaki iya karawa da spices da Kk so.irinsu ginger powder
Garlic powder da sauransu
Kafin a fara suya a bare maggi a daka asaka a container daban,a daka barkono a ajiye a gefe adaka dasu citta kanumfari masoro a jajjaga garlic a ajiye a yanka albasa dai dai yanda zakiyi amfani dashhi.
Bayan an Dora naman sai a zuba albasa su curry dasauran kayan kamshi sai a rufe baa bukatar zuba ruwa. Saidai In naman sa ne cos yana da tauri sai a zuba ruwa kadan.
A hankali zaaga mai ya fara narkewa a naman shikenan sai a fara suya zaki iya kara mai acikin naman za a iya soyawa da man kitse kawai..
Zakiyi ta juyawa har sai Kinga man ya fara kumfa toh yana nuni da naman ya fara soyuwa.
Kada a tsane naman da wurin a bari ya soyu sosai but kadda a barshi ya kone sai a juye naman a colender a tsaneshi shi gabaki daya. Aci dadi lfy.