GYARAN GASHI
gashi yana daya daga abinda yake karawa mata kyau , yana da kyau ki kasance gwana wajen iya gyaran gashinki.
GARIN HULBA
RUWAN LALLE
SABULUN HABBATUSSAUDA
garin hulba ki zuba acikin ruwan lalle ki dafa ya dafu sosai sannan saiki saukeshi kibarshi yayi sanyi sannan ki samun sabulun habbatussauda ki wanke.
kayin dashi sannan saiki samu wadannan mayikan.
man zaitun
man kwakwa
man alayyadi
man habbatussauda
man Sim Sim
zautun lauz
duk wadannan mayikan Zaki hadasu waje daya sannan kina shafawa akai kisamu kamar wata guda ko fiye da hakaβ¦..insha Allah gashinki zaiyi tsayi yayi laushi yayi baki.