BAYAR DA RUWA GA JARIRAI YAN KASA DA WATA 6 BAI HARAMTA BA SANNAN BA ILLA BACE A KIMIYANCE SANNAN BAI ZAMA DOLE BA AMMA AKWAI ABUN LURA DA KUMA ANFANIN HAKAN.

Ku ba Jariran ku Nono Zalla

Wata tamin Tambaya Shin menene fa’idar bayar da ruwa tsawan wata 6 ga JARIRAI sannan me hakan zai haifar idan aka bayar ko ana bayarwa.❓

A kimiyance Babu wata illa ko Matsala Dan anci gaba da bayar da ruwa ga Yara Yan kasa da watanni 6.

Saidai Kuma anfi bukata, Yafi Anfani, Anfi Samum Yara da cikakkar lfy idan aka kebesu daga bayar da ruwa har tsawan watanni 6.

Ruwan Mama Kashi 75% Ruwa ne, Sannan Yana dauke da wasu mahimman sanadarai wadanda suke taimaka wa gangar jikin Jarirai fiye da tinanin mu, Dan Haka Babu wani abunda Yafi ruwan Mama Anfani da saurin Gina jiki Kamar Ruwan Mama.

Illar da ake Samu ta bayar da ruwa shine, Bayar da ruwan na cika cikin yaro ya kasa Shan Mama Kan Kari, ya zama lokacin da duk za a bashi mama cikin ya cika da ruwa wadanda basu dauke da wadansu sanadarai na musamman.

Ruwan da muke Anfani dasu basuda inganci saboda Rashi ko talaucin dake addabar mu, Wasu itatuwa ake dafawa da sunan daurin jarirai sai ruwa suyi sati ana dafasu kullin ana ba jariri daga karshe matsaloli su biyo baya.

Duba Jikin Jinjiri Babu kwararan karfin Garkuwan jiki, Akwai dinbin Cutuka da ake iya dauka ta hanyar Ruwan shanmu, Yana da sauki Jarirai su kamu da Cutuka cikin kankanen lokaci fiye da babba. Yana daga cikin illolin kwayoyin cuta na Bacteria kamar cutar typhoid ashasu a ruwan da muke Anfani dasu.

Da dama Jarirai na zawo, wannan Bai rasa nasaba da Haduwar kwayoyin cuta na Bacteria ko protozoans da akafi saurin Samu cikin Ruwa.

Dan Tsakani da Allah Kauracewa Ruwan Yafi alkhairi ga JARIRAI fiye da abasu ko arika Anfani da ruwan musamman wadanda basuda cikakkar Tsafta.

Duk Jaririn da akai ma Exclusive Breastfeeding zaifi lfy, Kumari da Kuma nagarta.
Allah ne mafi Sani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *