BAYANI AKAN SIRRIN ZUMA


hakika ita zuma tana daga cikin manya-manya abubuwan da ake magani da su kuma itama kanta magani ce domin ya zo a cikin alkur’an mai girma
Inda Allah (S.W.T) yake cewa

wato yana futowa daga cikinta (ita zuma) wani abun sha wanda yake mai launuka daban-daban hakika a cikinsa akwai waraka ga mutane

zuma akwai

Fara
baka
da sauran color kuma tanada magani ko wacce daga cikin ta

haka nan yazo a cikin hadisin Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:-

na hore Ku da ababan waraka guda biyu (2) zuma da alkur’an (ibn majah da Hakim suka ruwaito wannan hadisi)

→ bayan haka an ruwaito cewa: wani mutum ya zo wajan Manzon Allah (S.A.W) yace : yaa Manzon Allah na zo ne in gaya maka cewa dan uwana yana fama da ciwon ciki, sai Manzon Allah ya ce jeka ka shayar da shi zuma, sai ya Tafi ya shayar da shi zuma amma bai warke ba, sai ya koma wajan Manzon Allah ya sake cewa jeka ka shayar da shi zuma, sai yaje ya shayar da shi, amma bai warke ba, sai ya komo wajen Manzon Allah sai Manzon Allah yace da shi hakika Allah yayi gaskiya, cikin dan uwanka yayi karya, jeka ka sake shayardashi zuma, da yaje ya sake shayar dashi zuma sai ya warke

wannan hadisi yazo cikin (bukhari da Muslim)

haka nan wannan yana daga cikin abun da ya kamata mu fa’idantu da shi cewa shi magani ba’a yi masa gaggawa, Ana so adinga mai-maitawa da haka har ubangiji ya kawo saukin cutar.

haka nan yana daga cikin sirrin zuma zaka ga yawan cin magani Ana cewa hada shi da zuma farar saka.

→ yana daga sirrin zuma in an haifi yaro ya Kai kamar wata hudu (4) kullum a dinga diga masa a baki sau uku (3) a Rana saboda ta Kara masa wayo da basira da kaifi hadda in ya girma. sannan tana sa kashinsa ya Kara kwari.

→ yana daga sirrin zuma mace mai jego ta dinga shan zuma a kullum itama sau uku (3) a Rana kafin ta haihu da bayan ta haihu saboda samun cikakkiyar lafiya da ita da yaronta..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *