Martanin gwamnan kano mai mulki a halin yanzu Dr. Adbullahi Umar Ganduje Akan Masarautu Hudu Da Muka Nada A Kano Mahadi Ka Ture, Kuma Mahadin Bai Bayyana Ba, Cewar Ganduje.
Martanin gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, akan batun masarautu, ya ce sabbin masarautu huÉ—u zama daram dam mahadi ka ture, kuma Allah ba zai kawo mahadin ba.
Kazalika, Gwamna Ganduje ya faÉ—i hakan ne da yake jawabi a taron bikin ranar ma’aikata, wadda gamayyar Æ™ungiyoyin Æ™wadagon jihar Kano suke shiryawa duk bayan shekara a gidan gwamnatin kano domin samarwa da hadin kan al’ummar jihar ta bangaren kawo musu zaman lafiya.
Gwaman abdullahi umar ganduje ya kara da cewa babu wanda ya isa ya ture wannan nadin na sarakunan da sukayi a jihar ko bayan basa kan mulki domin kuwa aiwatar da hakan tamkar rashin jawo zaman lafiya ne a tsakanin al’ummar jihar ta kano dama kewayenta baki daya.
Yayin da wasu daga cikin ‘yan kungiyar kwadagon suka kalli abin a wata fuska ta daban dangane da furucin gwamna mai ci a halin yanzu abdullahi umar ganduje zuwa ga sabon gwamna mai jiran gado wato abba kabir yusuf na jam’iyya (NNPP) sai dai ba zamu tabbatar ba sai munga hawan sabon gwamnan karagar mulki jihar.