Ganduje Ya Kafa Kwamitin Mikawa Abba gida gida mulki sabon gwamnan Jihar Kano abba kabir yayin da tsohon gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje Yafara shirye-shiryen kafa kwamitin miƙa mulki Ga Zaɓabben Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir .
Sanarwar da kwamishinan Yaɗa labarai da harkokin cikin gida Alh. Garba Muhammad yafitar, ta bayyana cewa Majalisar zartarwa Abdullahi Umar Ganduje ta Amince da kafa kwamitin miƙa mulki mai mutane 17 domin mikawa zababben gwamnan jihar, mulki.
Ana Kyautata zaton Gwamna Ganduje Zai kaddamar da kwamitin a ranar Talata da misalin karfe biyu na rana, a ɗakin Taro na Afrika House Dake fadar Gwamnatin Kano.
Akwai kuma kwamitin Mai mambobi 100 wanda zasuyi aiki a bangare na kundin tsarin mulki, ma’aikatu dakuma Hukumomi batare da ansamu wata matsala ba dangane da lamarin da zai gudana a lokacin cewar shugaban babban kwamatin mika zaben gwamnan jihar kano.
Garba Muhammad yace kwamitin zasuyi aiki cikin nutsuwa, dakuma jituwa da kwanciyar hankali batare da samun wani tsaiko ba yayin mikawa sabon gwamnan jihar mai jiran gado ragamar mulkin jihar kano cewar shugaban kwamitin mika zaben Alhaji garba muhammad.