Murja Kunya Ba Ta Dauki Neman Minin Auren Da Take Yi Da Muhimmanci Ba, Domin Na Nemi Aurenta Amma Tayi Tayimin Wala-Wala
Wani matashin dan siyasa kuma dan kasuwa mai mukami a Jam’iyar APC a karamar hukumar Chanchaga ta jihar Neja, Abubakar Turaki ya yi martani ga jarumar TikTok Murja, kan labarin da bayyana cewa tana neman mijin aure.
Turaki wanda a kwanakin baya muka wallafa maku labarin cewa yana sonta, ya ce tun sanda ya sanar da ita manufar sa akanta ta fara yi masa wala-wala har sai da ya gaji ya fita sabgar ta.
A cewar sa da da gaske take yi da lokacin da ya zo ta rungumi abun hannu biyu-biyu.
Ya ce tana yi ne kawai don daukar hankali da neman karin mabiya a shafinta.
Daga Nuruddeen Isyaku Daza