Ramadana 30 + Shawwal 6 = shekara guda.
“Azumin sittatu shawwal ba farilla bane, sunnah ne, idan kayi guda shiga acikin watan shawwal bayan kayi Ramadana, Allah zai baka ladan shekara guda ne”
“Ba wajibi bane, sannan kuma ba abin yin gasa bane, kuma ba abin yin riya bane, ka kiyaye don gudun kada kayi asarar ladansa a gurin Allah maɗaukakin sarki, shi sunnah ne wanda Allah yake bawa mutum ladan azumin shekara guda bayan ya azumci Ramadana”
“Manzon Allah ﷺ, yace: duk wanda ya azumci Ramadana, sannan kuma ya bishi da guda shida na shawwal, ya kasance kamar ya azumci shekara guda ne”
صحيح مسلم