ASÃRA MAFI GIRMA AWATAN RAMADÃN

TA FARKO.
Kai Baka Tsaya Anyi Sallar-Tarãwĩhi da Kai ba, Kuma Kai Baka Tãshi Cikin Dare Kãyi Wata Ibdah ba, Sa’annan daga Cin Abincin Sahur, Ka Koma Bacci Baka Sãmu Sallar-Asubahi ba.
LALLAI KA TAFKA ASÃRA

TA BIYU
Ramadãn Na Neman Tafiya, Amma Har Yanzu Baka Sauke (ALQUR’ÃNI) Koda Sau ɗaya ba, Gãshi Kai Bãbu Ruwanka da Zuwu Jin Tafsĩri, Kã Kãsa Zuwa Kõda Na Yini ɗaya, Kuma ‘Yar Sadakar Nan da Ake Kaiwa Masallaci Don Taimakon Marãyu, Ko Dabĩno da Ruwan Sanyi da Ake Kaiwa Don Sãmun Lãdan Masu Azumi, Babu Kai Aciki.
WANNAN BA ‘KARAMAR ASÃRA BANE

TA UKU
Ana Azumi Amma Kai Babu Ruwanka da Ambaton Allah, Sai Buga Game a Handset da Kallace-Kallencen Finãfinai da Gulmace-gulmace, da Musun-banza, Kuma alla-alla Kake yi Asha Ruwa Ka Kēta Alfarmar Daren Ramadãn da Sãbon Allah.
HM, ANYA KUWA!!!?

TA HU’DU
Asãra Mafi Girma da Zaka Tafka Shi Ne: A Sãmu Daren (Lailatul-Qadr) Yazo Ya Wuce Kana Shirga Bacci, Ko Kana (Night-Browsing) Wanda Meyuwu wa, Wannnan Azumin Shĩne: Na ‘Karshe A Rãyuwar ka Baka Sani ba.
ALLAH YA KYAUTA

NASIHOHI

Kana da Sauran Lokacin da Zaka Rĩbata, Kwana (14) Ko (15) Suka Rage Maka, Wanda Acikin Su Ne (Lailatul-Qadr) Yake, Kada Kace Sai A Goman ‘Karshe Zaka Neme Shi, A’ah, Ka Fara Rãya Dararen da Suka Rage Tun daga Yau Har Zuwa ‘Karshen Ramadãn dan Sãmun Tabbacin Muwãfaqa da Lailatul-Qadr.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *