Anyi Nasarar Kama Bazawarar Da Tayi Garkuwa Da Yar Cikinta A Jihar Kano Karanta Labarin – Interestingasf

Innalillahi wa’inna’ilaihi raji’un An Kama Bazawarar Da Tayi Garkuwa Da ‘Yarta A Kano Domin Ta Karbi Kudin Fansa Don Ta Samu Kudin Shiga Harkar Finafinan Hausa

Bazawarar mai suna Rahma Sulaiman an zarge ta ne da garkuwa da ‘yarta Hafsat Kabiru a Karamar Hukumar Madobi tare da neman kudin fansa a wajen tsohon mijin nata Alhaji Kabiru Sharada.

An ce tayi hakan ne dan samun kudin shiga harkar finafinai Haka kuma a gefe guda rundunar ‘yan sandan ta jihar Kano, ta gabatar da dillalan wiwi da kuma ‘yan fashi da makami a sahin gudanar da manyan laifuka na bomfai dake jihar kano.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan ta fara gudanar da tsattsauran bincike akan wannan lamari daya faru na samun nasarar cafke masu garkuwa da mutanan da kuma manyan laifukan safarar miyagun kwayoyi a fadin jihar da kewayenta domin kautar da matasa akan wannan laifuka na kayan maye.

Hakika irin wadannan laifuka na daya daga cikin manyan laifuka da matasan mu suke gudanarwa a halin yanzu domin kuwa hakan ya biyo bayan rashin kulawar da mafi yawan su basa samu daga wurin iyayen su, ko kuma abokanan arziki cewar rundunar ‘yan sandan ta jihar kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *