anfanonin nonon rakumi ga lafiya

Amfanin Nonon Rakumi a Jikin Dan Adam
Dabino da Nonon Rakumi na daya daga cikin abubuwanda Larabawa ke Girmamawa, kuma suna daga cikin abubuwanda suke baiwa Muhimmanchi Sosai.

Nonon Rakumi ba ana shan sa ne kawai ba, a’a yana kunshe da maganukka a cikinsa da yawa.

A Kasashen Larabawa sun yarda da Sinadiran da ke cikin dabino da kuma Nonon Rakumi Na matukar kara lafiya a jiki.

A yanda ake so anfi so mutum Yasha Madarar Rakumi a yadda aka debo ta kafin ta juye ta zama nono domin Idan ta zama nono zata Rage yawan sinadiran da suke cikinta.

GA DAI KADAN DAGA CIKIN CUTUKKAN DA YAKE MAGANI.

Nonon Rakumi Na dauke da sinadirai masu yawa a cikin sa wayanda ya kan samu wayannan sinadirai ne daga ire-iren itatuwan da take ci, wayanda suka hada da, Iccen Darbejiya (Neem tree), Lalle (heena), Zogale (Moringa), Kankana (watermelon) da dai sauransu.

Ciwon Suger (diabetes); Yawan Insulin dinda ke cikin nonon Rakumi wanda yawansa zai kai 52 micro unit/ml Yana taimakawa sosai wajen Rage Ciwon Suger.

CIWON DAJI (cancer) A wani bincike da aka gabatar a Jami’ar King Saud dake Saudi Arabia, da kuma Jami’ar Alberta da ke Canada sun gano cewa anti-tumor dake cikin Nonon Rakumi na taimakawa sosai wajen Kashe kwayoyin cutar Cancer a jiki.

CIWON HANTA A wani bincike da aka gabatar a watan September a shekarar 2012 da wasu likitoci ‘yan asalin Kasar Egyft da Spain su kayi sun Gano Shan Nonon Rakumi Yana da tasiri kwarai da gaske wajen Yaki da Cutar Ciwon Hanta Na Rukunin (Hepatitis C Virus (HCV)).

TAIMAKON GARKUWAR JIKI; Shan Nonon Rakumi Nada matukar amfani a jikinmu, domin Yana taimakawa kayan yakin dake cikin jiki.

WANKE CIKI DAGA DATTIN DAKE CIKINSA; antibacterial da kuma antiviral dake cikin Nonon Rakumi ba kadan suke taimakawa wajen wanke cikin mu ba daga Hayakin da muke shaqaba kamar na Sigari, Injin ko Mota/babur da sauransu.

DOMIN MATA KAWAI

Ga Maccen da take son Ni’ima a jikinta ta sami kwakwa da dabino ta jika su idan suka jika a markad’a su sai a tace sannan a kawo NONON RAKUMI sai a saka sugar a ajiye shi a cikin Na’ura mai sanyaye abu domin ya yi sanyi, sai ki rika diba a hakali kina shaa har tsawon Sati guda.

Godiya Ga Allah da Ya Albarkacemu da Samun Rakumi domin Mu mori abubuwa daga gareshi
Allah Ya sa Mu dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *