ANFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN

shidai zaitun mai albarka da kuma bada cikakkiya lafiya ajikin dan Adam, kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja , kamar yadda muka samu bayaninta.

haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah (S.A.W)

an karbo daga sayyadina umar yana cewa Manzon Allah (s.a.w) yace kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafashi ajikinku, hakika shi yana daga acikin bishiya mai albarka .
tirmizi ne ya ruwaito

GA WASU DAGA CIKIN AIKIN DA ZAITUN YA KEYI

CIWON CIKI

duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatussauda ya cakuda ya sha safe da yamma.

CIWON KAI

duk mutumin da yake ciwan Kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali daya da safe da Rana da dare in sha Allah zai samu lafiya.

CIWON HAKORI

duk mutumin da yake ciwon hakori sai ya samo ganya zaitun da ya”yan habbatussauda ya sakasu a cikin garwashi ya buda bakinsa hayakin ya dinga shiga. insha Allah

CIWON HANTA

duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan man bai tun cikin cokali daya da safe daya da Rana daya da dare , insha Allah

🫒 CIWON DADASHI

sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa dashi .

CIWON SIKARI

sai ya samu man zaitun da tsamiya yana hadawa yana sha kafin ya kwanta bacci, insha Allah.

CIWON ASMA

Sai ya samu ganyan zaitun ko ya’yan sa ya dinga turara wa, insha Allah zai samu sauki.

🫒 CIWON KODA

sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a rana insha Allah zai samu lafiya

🫒CIWON BAYA

sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda a ya kwaba ya dinga shafawa abayaninsha Allah.

CIWON RAMA

duk mutumin da yaga yana ramewa , to ya dinga shan man zaitun cokali uku insha Allah

🫒ZAZZABI MAI ZAFI

duk mutumin daya kamu da zazzabi mai zafi to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya sannan yana karanta ayatul kursiyyu sau (7) yana tofawa acikin yana shafe jikinsa dashi insha Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *