Yalo
Bincike da dama da masana suka gudanar ya nuna cewa yalo ya samo asali ne daga kasashen India da kuma Afirka, amma kuma yanzu ana noma shi a fadin duniya.
A Najeriya an fi noma yalon ne a yankin arewacin kasar inda akan kuma same shi a kasuwanni daban-daban a fadin kasar.
Za a iya cin danyensa wanda wasu sukan hada da soyayyiyar gyada ko su rika dangwalawa a hadadden garin yaji ko kuma soyayyiyar miya su rika ci.
Daya daga cikin abubuwan ban mamaki game da yalo shi ne yana fitowa a nau’uka daban-daban, wanda ya danganta da yanayi da kuma wurin da ake nomawa.
Yana kuma fitowa a launuka da kuma fasali da girma da kuma dandano daban-daban. Akan samu masu launkan fari, da ruwan goro, da kore, da algashi da dai wasu launuka.
A kudancin jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya akwai kabilar Baburawa da kan yi amfani da gauta wato daya daga cikin nau’in na yalo wajen abinci, su kan rika hadawa da tuwo suna gutsura suna ci.
Malama Adama Hassan wacce ‘yar kabilar Babur din ce da ke zaune a garin Biu na jihar Borno inda Baburawan suka fi yawa, ta shaida wa BBC cewa suna matukar muhimmantar da Yalo ko data, ko kuma gauta a matsayin cimaka.
”A ko da yaushe ba za ka taba rasa gidan Baburawa da gauta ko yalo ba, saboda muna hada shi da abinci, musamman tuwo, yana a matsayin miya ne, mu kan rika gutsurar shi mu hada da tuwo muna ci.”
Amfanin yalo ga lafiyar jikin dan adam
Galibin mutane na cin Yalo ne kawai don nishadi ko kashe yunwa ba tare da fahimtar irin dimbin amfanin da yake da shi a jikinsu ba.
A nan za mu duba amfanin yalo da kuma muhimmancin sa a jikinmu. Ba zai yiwu mu kawo duka ba, to amma za mu tsakuro kadan daga cikin amfaninsa:
Kamar yadda mujallar kiwon lafiya ta Medical News Today da ke Amurka ta wallafa, binciken da masana da dama suka gudanar game da yalon ya nuna cewa yana da matukar amfani ga lafiyar jikin dan adam kamar yadda ‘ya’yan itace suke da shi.
Rage kiba
Kamar yadda Mis Megan Ware wata kwararriya a fannin abinci mai gina jiki a Amurka kuma manomiyar kayan lambu ta wallafa a mujallar Medical News Today, yalo na da matukar amfani wajen rage kiba saboda yana kunshe da sinadaran da ke taimaka wa kona kitsen jikin mutum wanda kan sa a rage kibar.
Malama Husna Abubakar wacce ke zaune a garin Abuja babban birnin Najeriya ta shaida wa BBC cewa maigidanta wanda ke da kiba sosai ba ya rabuwa da sayen yalo saboda yana da yakinin cewa yana da matukar amfani wajen rage kiba.
”Na ga yana yawan sayen yalo kuma yakan saka ni in yanka masa kanana kamar yadda ake yanka su kankana in kawo masa a ko wane dare ya ji kafin ya kwanta,” in ji Husna.
Kare garkuwar jikin dan adam
Kamar yadda mujallar Healthline ta Birtaniya ta wallafa a wata majalar kiwon lafiya, sinadaran Anthocyanins, da nasunin da kuma flavonoids sinaran kashe kwayoyin cuta ne masu karfi da ke kunshe cikin yalo da kuma kan taimaka wajen bayar da kariya ga garkuwar jikin dan adam tare da kara inganta lafiyar jikin.
Sinadarin Anthocyanins na tainama wa wajen bayar da kariya daga yaduwar kwayoyin halittar da ke haddasa cutar kansa har ma da sauran cututtukan da kwayar cutar bacteria ke haddasawa.
lnganta aikin jijiyoyin jini
Yalo yana kunshe da sinadaran vitamin B kamar su thiamin, da niacin, da B6 da kuma pantothenic acid wadanda ke taimakawa wajen amfani da sinadaran fat da na protein; kana suna bayar da gudumawa mai amfani ga hanyoyin jijiyoyin sadarwar kwakwalwa.
Sinadarin vitamin B na taka muhimmiyar rawa wajen inganta kiwon lafiya. Yana taimaka wa wajen inganta aikin kwakwalwa tare da tabbatar da cewa hanyoyin jijiyoyin sadarwar kwakwalwa da na garkuwar jikin dan adam na aiki yadda ya kamata.
Karfi da lafiyar kashi
Saboda sinadaran minerals irin su folate, da manganese, da vitamin K, da magnesium, da vitamin da kuma Copper da yalon ke kunshe da shi, yana taimaka wa wajen kara karfi da lafiyar kashi.