A kasar IndiYa wadda a yau ita ce a sahun gaba ta fannin ayyukkan da suka shafi na kiwon lafiya da magani na zamani. Ya kasance al’ada a gare su domin tun a zamanin da sun kasance suna hada dabino da kuma madara a guri daya sai su sha da manufar inganta lafiya da karin kuzarin jiki da kuma magance wasu kananin rashin lafiyoyi da ke addabar su a yankunansu.
Shi dai dabino yana kunshe da wasu irin muhimman sinadirran da ke da dimbin alfanu ga jikin dan’adam, wadanda karancin wadannan sinadiran na iya haifar da wata illa ga jiki. ko baya ga haka, yana da wasu fili dake zama a matsayin maganin wasu cuttuka. A dalili da haka, dabino maganine ko baya ga zaman sa abinci.
A yayin da ita kuma madara take zama a matsayin protein da ake bukata dan ginin jiki, lafiyayyun kassa da hakora da kuma dai-daituwar aikin kwakwalwa.
Da irin dimbin sinadirran da ke a cikin dabino da kuma madara wannnn ne ya sa suka ninka duk wani maganin da za mu iya siya na Bature amfani. Domin sun za mu bitamin da ba wani hadi na kimiyar dan’adam a cikin su ballantana su haifar da wata matsala.
Dukan su suna kumshe da sinadirin Calcium wanda yake a gazawa kassan jiki, da kuma hakora.
Domin haka mai neman samun kwarin jiki zai iya fake amfani da madara da dabino.
Don shi ne ma ya sa ake danganta shi da kara kuzari wato yana hura karfin jiki.
Mai jin kasalar aiki ko saurin gajiya ko rashin karfi sai ya jarraba shan madara da dabino.
Hadin dabino da madara na taimakawa dan magance kananin cuttuka.
Kiba: Masu fama da rama maza ko mata marasa jiki kuma suke da bukata su yi kiba to sai su rinka shan madara tare da dabino.
Yana sa jiki ya samu wadata: Idan ana bukatar a jima ba a ci komai ba to sai a nemi dabino da madara kofi daya a sha, to a ranar fa sai dai a yi ta shan ruwa. kuma da zaran ka sha ruwa to za ka ji karfi kamar a lokacin ne ka ci abinci.
Yaran da yunwa (tamowa) ta kama ko wani da baya iya cin abinci ya koshi saboda da wani dalili
Amfanin Shan Madara Tare Da Dabino ga lafiyar jiki
