- Sanyin kirji:
A tauna saiwar zogale tare da citta kwara daya.
- Tsutsar ciki:
A tafasa saiwar zogale da jar kanwa a sha.
- Ciwon sanyi ga mata da maza:
A tafasa saiwar zogale da kwara daya na tafarnuwa a sha sau biyu ga wuni tsawon kwana uku.
- Yawan ruwan maniyi ga namiji:
A gauraya cokali daya karami da sachet daya na madara.
- Tarin sanyi ko Mura: A gauraya garin saiwar zogale da zuma a sha cokali daya a kullum da safe tsawon sati daya.
- Rage nauyi ko qiba:
A tafasa saiwar zogale da lemun tsami daya a tace a sha bayan an karya sau daya a kullum
- Zafin fitsari :
A tafasa saiwar zogale da kanumfari a aha sau uku safe da rana da yamma.
- Ciwon sugar:
A rinka cin garin saiwar zogale a cikin abinci.
- Qazuwa:
A gauraya cokali daya na garin saiwar zogale da man zaitun a sha
- Ciwon daji a cikin baki:
A tafasa saiwar zogale a marmasa gishiri a kurkure baki dashi a kullum sau uku, safe da rana da yamma
- Ciwon yatsa na Dankankare :
A gauraya kwata na karamin cokali na garin saiwar zogale da na lalle a dorawa yatsan dake ciwo.
- Matsanancin ciwon kai na zafi:
A yi hayakin saiwar zogale da garin habba.
- Ni’ima ga mata:
A tafasa saiwar zogale a tace ruwan misalin kwara daya na karamin cup sai a zuba rabin gwangwanin madara a sha.