AMFANIN LUBBAN ZAKAR GA LAFIYAR AL’UMMA.

AMFANIN LUBBAN ZAKAR GA LAFIYAR AL’UMMA.

فوائد اللبان الذكر

 1. Ana amfani da Lubban Zakar wajen warkar da ciwo ko rauni. Domin kare kai daga kamuwa da cutar ‘Tetanus’, ana iya sanya shi a ciwon kuma ba shi da wata illa.
 2. Lubban Zakar yana dauke da sinadaran ‘antiseptic’ da kuma ‘disinfectant’, wadanda ke kashe kwayoyin cuta da kuma fitar da hayakin da ya shiga cikin ciwo lokacin da mutum ya kone.
 3. Matsalolin Baki.

Wannan sinadarin na ‘antiseptic’ da ke cikin Lubban Zakar yana taimakawa wajen matsalolin numfashi da ciwon hakori, kaikayin baki da sauran matsalolin baka. Don haka yana da kyau mutum ya samu sinadarin goge baki wanda yake dauke da Lubban Zakar a ciki ko kuma ka hada shi da kanka, don gige baki.

 1. Sinadarin ‘Astringent’ da ke cikin Lubban Zakar yana da amfani da yawa. Yana karfafa dasashin baki, yana kara yawan gashi, kyautata fatar la66a, karfafa qasusuwa, gyara hanji, bude kofofin jini, sannan yana maganin zubewar gashi da kuma hakora na yara.
 2. Saukaka zuwan Jinin Al’ada.
  Lubban Zakar yana rage wasa da 6ata lokacin da jinin al’ada yake yi wa mata. Haka nan yana maganin cututtukan da suke da alaqa da zuwan jinin al’ada kamar ciwon mara, ciwon kai da dai sauransu.
 3. Lubban Zakar yana cire wani sinadarin ‘Gas’ mara amfani daga jikin mutum. Fitar wannan gas daga cikin hanji yana rage hadarin kamuwa da ciwon ciki, ciwon mara, cututtukan cikin mahaifa, ciwon kirji, yawan gumi da dai sauransu.
 4. Yana rage dabbara-dabbara ajikin fata. In ana shafa Lubban Zakar ko ana shakarsa, yana saurin warkar da tabo da dabbara-dabbaran da fata tayi sakamakon warkewar wani ciwo ko kuraje. Yana 6atar da tabon Nankarwa, wajen da aka yanka yayin tiyata da kuma budewar fata yayin goyon ciki.
 5. Lubban Zakar yana taimakawa wajen sarrafa abinci acikin jiki, domin yana dauke da sinadaran ‘digestive properties’ wadanda ba su da wata illa, yana taimakawa sarrafa abinci kamar yadda magunguna suke yi, domin yana dauke da dukkan sinadaran da ake bukata domin sarrafa abinci ajikin danAdam.
 6. Maganin cutar Daji wato Cancer. Sinadarin ‘boswellic acid’ da ke cikin Lubban Zakar yana taimakawa wajen hana kamuwa da cutar Cancer. Ana kuma iya mafani da shi wajen hana cutar kansar fata ko kansar nono yaduwa zuwa ga sauran sassan jikin mutum, haka nan bincike ya tabbatar da cewa Lubban Zakar yana maganin kansar mahaifa.
 7. Lubban Zakar yana hana saurin bayyanar tsufa ajikin mutum, saboda yana dauke da sinadaran da ke maganin tabban fata, da zafin rana, da tattarewar fatar ido sannan yana dame dukkan fatar da ke jikin mutum, sannan yana maye gurbin sinadarn da suka gama aiki a jikin mutum da wadansu sababbi.
 8. Saukaka fitar fitsari. Lubban Zakar yana taimakawa wajen saukaka fitar fitsari ajikin mutum da kuma nauyin da ruwa mara amfani yake sakawa, tage kiba da kuma dukkan sinadarai marasa amfani ajikin mutum sannan kuma ya rage hawan jini.
 9. Saukaka numfashi. Yana maganin tari kuma yana fitar da dukkan dattin da ke cikin ga6o6in numfashi da kuma huhu. Haka nan yana maganin cushewar hanci yayin mura. Baya ga nan kuma yana daidaita yanayin jiki idan yay kasa ta dalilin sanyi.
 10. Rage gajiya. Lubban Zakar yana maganin gajiya, wahala, gajiyar kwakwalwa da kuma ruhi. Yana rage zafin zuciya, fushi da kuma 6acin rai musamman ga maza.
 11. Wanke kwakwalwa. Tun a gargajiyance, an gano cewa Lubban Zakar yana bude kwakwalwa da kara basira. A binciken zamani kuwa, an gano cewa wadansu 6eraye da aka baiwa iyayensu Lubban Zakar su ka sha, lokacin suna goyon cikinsu, yayan sun samu basira da wayo, fiye da yadda sauran 6eraye suke da su.
 12. Lubban Zakar sinadari ne mai muhimmanci kwarai da gaske wajen karya sihiri da sauran matsalolin Aljanu. Yana maganin jinnul Ashiq wato Aljani mai saduwa da matan mutane sannan yana maganin Jinnus sihr, wato Aljani mai shiga jikin mitum ta hanyar sihiri.
 13. Ana amfani da Lubban Zakar wajen magungunan mata kamar hayakin tsuguno, matsi da sairan kayan ni’ima.
 14. Lubbabn Zakar sinadari ne mai karfi wajen kara ingancin namiji wajen kwanciyar aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *