Amfanin koren ganyen shayi

Koren ganyen shayi na da amfani a jikinmu domin shansa na kara lafiya da kuma kara kyan fata. Za a iya shafa ganyen shayin a fuska. Koren ganyen shayi na kare fata daga saurin tsufa. Bayan haka, yana kare jikinmu daga cututtuka da dama. Yawan shan koren ganyen shayi na sanya a ga mutum kamar saurayi koda ya hada shekaru. Hanyoyin da za a iya amfani da koren ganyen shayi.

Za a iya amfani da koren ganyen shayi a fuska

A kan sanya wannan ganyen a cikin man shafawa da dama. Domin ganyen na kunshe da sinadarin bitamin C da A da kuma E. Amfani da ganyen na rage maikon fuska kuma fuskar ta yi santsi yadda ko alamar kuraje ba za a gani ba. Za a samo mayonnaise sai a dibi cokali uku daga ciki.

Sannan dakakken ganyen shayi. Za a rika shafawa a fuska ban da gefen idanu. Sai a bar shi na tsawon minti 20 sai a wanke da ruwan dumi.
Amfani da koren ganyen shayi na rage warin numfashi.

A tafasa ganyen shayi. Bayan haka, sai a jira na tsawon minti 30. Sai a rika amfani da shi wajen wanke baki. Yin hakan na hana datti zama a kan hakora. Kuma zai kare bakin daga wari.

Shan shayin na rage kiba; ana iya shan shayi safe da yamma domin rage maikon jiki.

Koren shayi na rage tumbi ga macen da ta taba haihuwa da wadda ba ta taba haihuwa ba.

Shan ganyen shayi marar sukari akalla sau biyar a rana na matukar rage tumbi ga mata musamman matar da ta taba haihuwa. Gara a gyara tunda ba a kwalliya da tumbi. Yana da kyau a jure na tsawon wata biyar za a yi matukar mamakin yadda tumbi zai shanye.

Ganyen shayi na magance ciwon ido.

A sanya ganyen shayi a gidan sanyi na tsawon minti biyar sannan a rika dorawa a kan idon har sai ya narke. Yana rage ciwon ido mai zafi.
Yana gyara fuska.

A samu koren ganyen shayi sannan a zuba burbudin a cikin zuma sai a rika shafawa a fuska na tsawon minti ashirin akalla sau biyu a rana

safe da yamma. Yin haka na magance fesowar kurajen fuska.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *