Amfanin kanunfari Guda 7 ga lafiyar Dan Adam

Mafi yawan Mutane Suna Kallan Kaninfarine kawai domin Sanyawa a shayi ko kayan kamshi irin na yaji da makamantansu.

Amfaninsa bai takaita iya nan kawai ba, domin yana maganinabubuwa da dama kamar

CIWON HAKORI: dandaqashi akeyi a lika cikin hakirin.

BASUR: jikashi ake ya tsumu, kullum sai asha cokali uku da safe da dare.

MAGANCE MATSALAR WARIN BAKI: jikashi ake da lemon tsami da garin habbatsusauda adinga kuskure baki dashi kullum da safe da rana da dare.

WANKE JINI: jikashi ake da tsamiya adinga sha sau daya Kullum.

MAGANAR LARURAR SIKILA:Tafasashi akeyi tare da Zogale adinga shan ruwan ana cinye ganyen.

( KORAR MACIZAI DAGA GURI:Yadda mata Suke turaran kamshi, idan aka Dan zuba ko gudabakwai ne acikin garwashin, to macizai basu zama agurin, idan akwai suma sai sunyi kaura awajan.

MAGANCE MATSALAR WAHALAR HAIHUWA: Kullum me ciki ta dinga Samun kaninfari tana taunawa kamar gudu uku tana hadiye ruwan yawun bakinta idan ta tauna.

Da yardar Allah ba zatayi doguwar nakudaba ko kuma ace ta wahala wajan haihuwa.

Ya Allah ka cigaba da wadatamu da lafiyar Zuciya da gangar jiki gaba daya.

A yi sharing din wannan post din don sauran yan uwa da ba su yi like din page din ba su gani su karu suma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *