Amfanin Kankana ga lafiyar jiki da ta Iyali

Kankana uwar ruwa gashi komai nata nada amfani a jikin dan-Adam, ga wasu daga cikinsu kamar haka:-

  1. Kankana na dauke da sinadarin “Lycopene” wanda yake kauda kwayoyin cutar daji
  2. Kankana na samar da kariya daga ilollin zafin rana da kuma haske
  3. Masu yawan shan kankana tana ingata lafiyar su domin da wuya su kamu da cutar Asthma saboda kankana na dauke da sinadarin “Vitamin C”
  4. Kankana na samar da kariya ga cututtukan da suka shafi zuciya
  5. Ya’yan kankana nada mai, wannan man na taimakawa domin gina jiki da ingantashi
  6. Ya’yan kankana na dauke da sinadarin “amino acids” wannan sinadarin na karawa Dan-adam lafiyar jiki da karfi da kuzarin jima’i
  7. Ya’yan kankana na kara kaifin tunani
  8. Idan mutum yayi rashin lafiya yana bukatan kankana domin kuzarin sa ya dawo
  9. Kankana tana dauke da sinadarin dake bada kariya da rage cutar hawan jini
  10. Uwargida zaki iya yin juice dinta domin inganta lafiyar ki da kara miki ni’ima ingantacciya dana mai gida kai har ma da yara tana gyara su,

Kankana kenan uwar ruwa, kariya, sanya nishadi, uwargida kada ki bari a barki a baya domin kankana nada matukar amfani a gare mu baki daya ki hanzarta ki koyi hanyoyin sarrafa ta domin amfanin ki da na iyalin ki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *