A wannan rana za mu kawo mu ku bayani dangane da amfanin Hulba ga lafiyar bil’adama. Hulba kamar yadda mu ka san ta, kalma ce ta larabci, da harshen turanci kuwa ana kiran ta da ‘Fenugreek’. Hulba wani tsiro ne mai matukar amfani ga lafiya, kuma shekaru aru-aru da su ka shude al’umma ke amfani da ita don samun waraka daga wasu matsalolin lafiya.
Jama’a na amfani da ganye da kuma kwayar hulba wajen samar da magunguna tun a shekarun da su ka gabata. Hulba ta shahara a kasashe da dama a duniya, sai dai anfi samun ta a wasu daga kasashen Larabawa musamman kasar Misra, sannan ana samun hulba a kasar Sin da kuma Indiya.
A kasar Indiya su na kiran ta da, ‘Methi’ a yaren Hindu, a yaren Telugu na Indiyan kuwa su na kiran ta da ‘Menthulu’. Wani bincike da wata kafar yada bayanai ta yanar gizo ta wallafa, ya nuna cewa, Hulba ta shahara a kasar Indiya saboda amfaninta ga lafiya, ta yadda za ka iya kiran ta gidan kowa da akwai.
A al’adance, mutanen kasar Indiya na amfani da kwayar hulba a matsayin wani mahaÉ—in samar da magunguna, baya ga amfani da su ke da hulba don samar da wasu hade-hade na inganta lafiyar jiki, da kuma yadda su ke amfani da hulba don kula da lafiyar gashi.
Sai dai, binciken zamani na kwanan nan da masana su ka gudanar a kan hulba ya nuna cewa, za ta iya samar da magunguna da hade-haden inganta lafiya daga hulba, fiye da yadda jama’a su ka sani a baya. Daga cikin amfanin hulba ga lafiya da masanan su ka gano, har da taimaka wa ma su ciwon siga, ciwon ido, gyaran gashi da fata. Hakanan, ana amfani da hulba kan matsalar basir, matsalolin ciki da sauran su.
Yanzu ga bayani daki-daki kan amfanin hulba ga lafiyarmu:
Hulba na hana Bushewar fata; Bincike ya tabbatar da cewa, yin amfani da hulba na hana bushewar fata. Saboda haka duk mai fama da wannan matsala ta bushewar fata zai iya amfani da hulba don maganin wannan matsala.
Yadda za a yi shine ya samu garin hulba, ya kwaba ta da ruwa, amma kwaben ya yi kauri, sai ya shafa a fuskarsa, ya bar shi tsawon rabin sa’a, daga bisani ya wanke.
Hulba na maganin Basir; Ga mutanen da ke fama da wannan matsala ta basir, za su iya amfani da hulba su samu sauki cikin yardar Ubangiji. Za a samu hulba a dafa, sai a sauke, idan ta huce sai a zuba zuma, ake sha, musamman awa guda kafin a kwanta barci.
Hulba na maganin rashin ruwan nono ga mai shayarwa; A wasu lokutan, akan samu mace ta haihu amma sai ta samu karancin nono. Yin amfani da hulba zai samarwa da mai shayarwa ruwan nono, kuma zai taimaka wajen girman jaririnta.
A kasashen da ke nahiyar Asia, mata kan yi amfani da hulba don maganin matsalar rashin ruwan nono ga mai shayarwa. Masana sun ce, hulba na taimakawa wajen samar da ruwan nono ga mata ma su shayarwa ne, sakamakon wani sanadari mai suna ‘phytoestrogen’ da ta ke kunshe da shi. Ana samun wannan fa’ida ta hulba ne, ta hanyar shan ta cikin ruwan shayi.
Ko kuma, mace ta samu ‘ya’yan hulba ta dafa da man Ridi ta dinga ci har tsawon kwana 3, sannan ta ke shafa man hulbar a nononta, In Allah Ya so za’a samu biyan bukata. Domin kuwa za ta samu ruwan nono da zai wadatar da jaririnta, kuma ya kasance cikin koshin lafiya.
Amfani da hulba na rage ‘kwalastaral’ (kitse marar kyau) a cikin jini; Bincike ya tabbatar cewa, yawan amfani da hulba na taimakawa wajen rage yawan kwalastaral a cikin jini, musamman marar amfani da ake kira ‘bad’ cholesterol ko kuma LDL’ da turanci.
Ana amfani da hulba wajen maganin cushewar ciki; Hulba na taimakawa wajen saurin narkewar abinci, sakamakon haka sai ta ke maganin cushewar ciki. Duk ma su fama da matsalar cushewar ciki ko kumburin ciki sakamakon rashin narkewar abinci sai ya dimanci amfani da hulba, zai samu afuwa, insha Allahu.
Mata na amfani da hulba don karin ni’ima; Idan mace na fama da rashin ni’ima ko bushewar farji, za ta iya samun hulba ta yi amfani da ita, kuma insha Allahu za ta dace. Yadda za ta yi amfani da hulba don karin Ni’ima shine, ta samu ‘ya’yan hulba da kanumfari da ‘ya’yan habbatus-sauda da kuma Zumarta mai kyau.