Amfanin goruba Ajikin Dan-Adam

Amfanin goruba Ajikin Dan-Adam

 • Maganin basir
 • Maganin Hawan jini
 • Maganin ciwon qoda
 • Ciwon hanta
 • Ciwon shawara
 • Ciwon mara
 • Ciwon sanyi
 • Ciwon taipot (typhoid)
 • Ciwon maleriya(malaria)
 • Zafin jiki
 • quraje
 • Kashin jini

Yadda ake amfani dashi za’a samu goruba dadama ayi garinsa ko asayo garinsa

mai fama da ciwon basir da typhoid zai zuba garinsa cokali 2 da garin arrabi cokali daya acikin madara yariqasha har sati daya.

Mai fama ciwon sanyi da ciwon mara ya samu garin goruba cokali daya da garin tafarnuwa cokali daya ya zuba a madara yasha sati biyu

Mai fama da ciwon malaria da zafin jiki ya samu goruba cokali biyu da garin rai dore cokali daya da garin zunzuna cokali daya ya hada ya zuba a madara yasha sati daya,

Mai fama da ciwon hawanjini da qoda yasami garin goruba cokali uku da garin ganyen dankali cokali biyu da garin zogala cokali biyu da garin ganyen tumatiri cokali biyu ya zuba a madara yasha sati uku

Mai fama da ciwon hanta ya samu garin goruba cokali biyu da garin kalkashi cokali biyu azuba aruwan zafi Asha har sati uku .

Mai fama ciwon quraje ya sami ya sami garin goruba cokali daya da garin goga masu cokali daya ya hada da madara yasha sati daya

Mai fama da ciwon shawara ya sami goruba cokali biyu da garin mujirya(jinjirya) cokali biyu da garin tafarnuwa cokali daya Asha da madara sati daya

Mai fama da kashin jini ya sami garin goruba cokali uku da garin sabara cokali daya da garin ganyen dorawa cokali daya Asha da madara sati daya

Abin lura, madaran shanu kuma kafi daya ne karya wuce, daga dandalin magungunan mata

A daure arika share (turawa/jama’a) domin Amafanuwan Al-umma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *