AMFANIN GARIN SASSAKEN MARKE

Ko shakka babu.Jikin mutum yana samun ginuwa ne. da samun
kariya daga matsaloli ta dalilin amfani da tsirrai, ko
Bishiyoyi, da kayan maramari.
Hakika wannan bishiya ta marke, dukkan jikinta
yana da amfani.

  1. SAIWAR BISHIYAR MARKE:

Ana dafa ta da jar kanwa ana yi wa mai mutuwar
barin jiki gashi da ruwan maganin mai dumi, sau 2
a rana, tare da shan ruwan maganin rabin kofi sau 2
a rana tsawan kwana 14 za’a samu lafiya da yardar
Allah.

  1. SASSAKEN MARKE:

Idan aka hada shi da Jan kajiji aka nika suka zama
Gari
A dinga shan cikin karamin cokali da ruwan dumi
ko shayi, sau 2 a rana tsawan kwana 7 yana
maganin tari,
asthma, kurajan huhu,
taruwar ruwa a cikin huhu,
daskarewar majinar kirji,
Numfashi da wahala,
sanyin jiki,
rashin karfin jiki,

  1. ZUBA GARIN SASSAKEN MARKE DA SASSAKEN TSAMIYA CIKIN NONO A RINKA SHA

Yana magance

  • Zazzabi,
  • kasala,
  • Ciwan jiki,
  • Ciwan ciki,
  • Amai,
  • Gudawa,
  • Da kuma sassauta ciwon daji
  • Allah yasa adace

A turawa yan uwa su amfana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *