Amfanin Ganyen Gwaiba Ga Lafiyar Dan’adam

Kasahe da dama kama daga Japan da United State da Indiya da Egypt da Chana da ma fi yawan kasashen bakaken fata na Nahiyar Afirca sun dauki shekaru tun a zamanin kakanni zuwa yau suna cin gajiyar maganin da ganyen gwaiba ke yi.
Binciken masana sirrin tsirran itatuwa dana kimiya sun jima da bada tabbaci na musamman kan alfanun ganyen gwaiba. Ganyen yana dauke da wasu irin muhimman sinadarai masu zaman maganin wasu cuttuka a wannan zamanin.

Ga Kadan Daga Cikin Su

Ganyen gwaiba na maganin gudawa kama daga manya da kuma kanana, gudawar na sanadin cin abinci ne ko wani abin sha da ya lalata ciki ko kuma shigar wasu kwayoyin cuta da makamancinsa.

Idan kananan yara musamman wadanda ke shan mama sun kamu da gudawa to sai ita uwar ta nemi ganyen gwaiba ta wanke da kyau sai ta sabeta sai ta saka ruwa ta tafasa sai ta tace ruwan ta sha rabin kofi da safe da kuma rana bayan awa daya ko biyu sai a baiwa yaro mama ya sha, in sha Allahu gudawar za ta tsaya. Haka idan uwar ce ta kamu da gudawa ko duk wani mutum babba shi ma zai iya yin haka in sha Allahu zai ji dadin jikinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *