AMFANIN GANYEN BISHIYAR KUKA A JIKIN DAN ADAM

:

Ganyen kuka wanda a Ingilishi suke kiransa da (baobab) na dauke da sinadarai da dama wadanda ke inganta lafiyar jiki.

Ga sinadaran da ganyar bishiyar kuka na dauke da su:

 • Vitamin C
 • calcium
 • phosphorus
 • carbohydrates
 • fiber
 • potassium
 • protein
 • lipids
 • magnesium
 • zinc
 • sodium
 • iron
 • lysine
 • thiamine

Yana inganta lafiya ta hanyoyi da dama, haka kuma yana magance matsaloli iri-iri da ka iya samun mutum na yau da kullum. Ga kadan daga cikin

Ga kadan daga cikin amfanin da ganyen kukar ke da shi:

1- Yana magance tari da taruwar majina a kirji.
2- Yana rage yawan zufa kamar yadda su turarukan zamani ke yi.
3- Yana rage ciwon Asthma da na koda da na madaciya.
4- Yana rage gajiya da kumburi.
5- Yana rage radadin cizon kwari.
6- Yana magance tsutsar ciki.

Bayan wadannan wata bincike ta nuna ganyar kuka tana da wassu amfanin kamar haka:

 • Zazzabin maleriya
 • Tarin fuka TB
 • Tana ingana garkuwar jiki
 • Tana Æ™ara jini a jiki
 • Tana maganin gudawa
 • Tana maganin hakori
 • Tana maganin ulsa
 • Tana rage Æ™iba

Sai dai kuma busar da ganyen kuka a rana kamar yadda muke yi na rage masa sinadarai da a kalla kaso 50 cikin dari. An fi son a busar a inuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *