Amfanin cin Karas A Jikin Dan’adam

Amfanin karas dangane da lafiyar dan’Adam da kuma samun kariya, daga cututtuka musamman irin cutar daji, inda take shiga cikin jikin mutum tana lalata mahiifa, dalilin sanadiyyar lalacewar mahaifa kuma yana sabbaba kamu da ciwon daji
Karas yana dauke da wasu sinadarai masu yawan gaske, kamar Mangenes, Aion, Calsiom, Phosphorus, Better Carotene, Alpha carotene, yana kuma dauke da cikakken Sinadarin Bitamin A, da Bitamin C, da Kuma Maadinin Anti-odidants, wanda yake bama jikin dan’Adam kariya da Kuma garkuwar

  • Karas yana kara lafiya idanu sosai ta fuskar kara gani da kuma hasken idanu
  • Karas yana magance tare da bada kariya ga kamuwa da cutan daji
  • Kamar yadda Likitoci masana suka bayyana cewa, a duk lokacin da aka kunna kukan gas a cikin gida ko aka kunna wutar icce ko aka kunna fitila ko kuma taba to dole sai an samu cuta ta kewaya wannan gurin, kuma ita ce take shiga cikin jiki tana lalata mahaifar dake cikin jikin mutum, wannan dalili yana daya daga cikin abin da yake haddasa wa asami cutar daji. Don haka masu gida ku rika saya wa iyalanku karas suna ci, ko kuma a yi garin sa ana sha da zuma ko ruwan shayi. Ko a rika sakawa a cikin abinci ko a rika nikata ana shan ruwanta ko a dafa
  • Garin Karas idan mai cutar daji yana shan to yana kone cutar na daji in sha Allah
  • karas yana dauke da cikakken sinadarin Bitamin A, dukkan 100 gram na karas ya tattaro 8.285 micro gram na better carotene. Kuma yana dauke da pulapuniad cikakke wanda yake aiki wajen kare fatar jiki, da kuma matsalar hunhu da kare su daga cututtutka wadanda ake shakar su ta hanyar odygen zuwa cikin jiki
  • Karas yana yakar ciwon zuciya, sa’annan yana da asiri ga masu fama da ciwon zuciya da kuma ciwon hawan jini
  • Karas yana dauke da sinadarin mai saka wajiki karfi sosai
  • Karas yana baiwa hanta kariya daga cututtutka wadanda suke kewaye da ita
  • Yana kara lafiyar hakora da kuma dasashi. Yana hana Tsutsar hakori. Yana taimakawa wajen magance warin baki
  • Yana gyara fatar jiki. Yana hana fitowar kuraje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *