AMFANIN BAWON LEMU

bawan lemu yakasance wani Abu mai mahimmancin gaske ,yana dauke da sinadarin calcium da vitamine A .
…za’ayi garinshi bayan ya bushe domin magance matsalar fata, zubar gashi,ciwon oda,Dandruff,face powder,diabetes, ciwon sugar,da matsalar digestion.

Idan kinada matsala na zuban gashi ko dandruff:zaki samu garin bawan lemu ki kwaba da ruwa sai kibarshi har tsawan awanni ashirin da hudu sai kishafa a gashinkin kuma ki tabbatar ya taba har can cikin kanki..insha Allah idan kina cigaba dayin haka,zaki nemi dandruff ki rasa.

Idan gashinki yana lalacewa ko zubewa,zaki kwaba garin lemun tareda Zuma da wani mai Wanda yakeda mahimmancin gaske wato tea tree oil.sai kidinga shafawa aduk lokacinda kika wanke gashi ko kuma kikazo gyara.

Ana hada garin lemun tsami ko garin bawan lemun zaki tareda Zuma domin magance matsalar digestion, ciwon ciki da ciwon sugar

MAI fama da matsalar sanyin Mara,warin gaba Na’iya amfanida garin lemun sai a kwaba da garin kanumfari dakuma Zuma ,sai adinga tsarki dashi.yana karawa gaba lafiya,yanasa matsi ,sannan yana Kara jin dadi.

Duk Wanda yake fama da basir kowane irine sai yahada garin bawon lemun da zuma cikin ruwan shayi babu madara ,sa’annan sai yasha kamar sau biyu safe da yamma Har asamu lafiya.

Allah yasa adace

A turawa yan uwa su amfana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *