Amfani da koren ganyen shayi Wajan Gyaran Fata

Ganyen shayi na da amfani a jikinmu domin shan sa na kara lafiya da kuma rage gautsin fata.

Kowane ganyen shayi na da nasa amfani a jiki, amma koren ya fi mahimmanci. Za a iya shafa ganyen shayin a fuska.

Koren ganyen shayi na kare fata daga saurin tsufa. Baya haka, yana kuma kare jikinmu daga cututtuka da dama.

Yawan shan koren ganyen shayi na sanya a ga mutum kamar saurayi ko ya yi shekaru.

Hanyoyi da za a iya amfani da koren ganyen shayi.

Amfani da koren ganyen shayi

na rage warin baki: A tafasa ganyen shayi. Bayan haka, sai a jira na tsawon minti 30. Sai a rika amfani da shi wajen wanke baki. Yin hakan na hana dauda zama a kan hakora. Kuma zai hana bakin wari.

Shan shayin na rage kiba: za a iya
shan shayi safe da yamma domin rage maikon jiki.

Koren shayi na rage tunbi ga macen da ta taba haihuwa da wadda ba ta taba haihuwa ba.

Shan ganyen shayi mara sukari akalla sau biyar a rana na matukar rage tunbi ga mata, musamman ma macen da ta taba haihuwa.

Gwara a gyara tunda ba a kwalliya da tunbi. Yana da kyau a jure na tsawon watanni biyar za a yi matukar mamaki da yadda tunbi zai baje.

Ganyen shayi na magance ciwon
ido: A sanya ganyen shayi a firinji na
tsawon minti biyar, sannan ana daura
a kan idon har sai ya narke. Yana rage ciwon ido mai zafin nan.

Yana gyara fuska

A samu koren ganyen shayi sannan a zuba burbudin a cikin zuma sai a rika shafawa a fuska na tsawon minti 20, akalla sau biyu a rana, safe da yamma. Yin hakan na magance fesowar kurajen fuska.

Za a iya amfani da koren ganyen
shayi a fuska; Akan sanya wannan ganyen a mayuka da dama na shafawa. Domin ganyen na kunshe da sinadarin Vitamin C da A da kuma E. Amfani da ganyen na rage maikon fuska kuma fuskar ta yi santsi yadda ko alamar kuraje ba za a ji ba.

Za a samo mayonnaise sai a dibi cokula uku. Sannan a zuba dakakken koren ganyen shayi. Za a rika shafawa a fuska ban da gefen idanu. Sai a bar shi na tsawon minti 20, sai a wanke da ruwan dumi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *