Amfani 10 da kukumba ke yi a jikin dan adam Wanda ya kamata ku sani

Amfanin cin danyen gurji suna da yawa kamar yadda wani masanin ilimin hada magunguna mai suna Gurama Gurama

A. ya bayyana. Cucumber na daga cikin dangin kayan marmari daga cikin rukunin Cucurbitaceae kuma tana kunshe da ruwa mai tarin yawa. Gurama yace cucumber na taimakawa wajen rage rashin ruwa a jiki ballantana a lokutan zafi.

“Mutane na cin cucumber ne a matsayin kayan lambu amma tana cikin kayan marmari.

Ana amfani da ita a cikin wasu kayayyakin gyaran fata. Kayan marmari ce kamar kankana da kabewa.

” In ji shi. Tana kunshe da sinadaran Vitamin irinsu A, B, C, K, potassium da Manganese wadanda ke da matukar amfani a jikin dan Adam.

Ga wasu daga cikin amfanin cucumber kamar yadda Gurama ya bayyana.

Tana taimakawa wajen narkewar abinci.

Tana taimakawa wajen rage kiba.

Tana taimakawa wajen karin lafiyar kwakwalwa.

Gurji na warware gajiyar jiki.

Gurji na kunshe da sinadaran vitamin B1, B5 da B7.

Tana hana warin baki

Gurji na hana ciwon koda.

Gurji na maganin ciwon ido.

Gurji na taimakwa wajen daidaituwar karfin bugawar jini daga zuciya.

Akwai yiwuwar gurji ta kare mutum daga cutar sankara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *