ALAMOMIN DAREN LAILATUL QADRI

Daga Wasilatu(RA) yace Manzon Allah (SAW) Yace Daren Lailatul Qadri dare ne mai haske baya da zafi baya da sanyi ba a jifa da tauraro a cikinsa daga cikin alamarsa shine rana zata fito a washe gari ba tare da tartsatsi ba.

(Sahih Jami’u Saghir 5348).

Daga Ibn Abbas (RA) yace Manzon Allah (SAW)  Yace “Daren Lailatul Qadri dare ne mai natsuwa a sake ba zafi ba sanyi, rana zata wayi gari tana mai rauni.

(sahih Jami’u saghir 535).

ME AKE FADA A DAREN LAILATUL QADR?

عنْ عَائِشَةَ رَضِيَ الله عَنْهَا قَالَتْ : قُلْتُ : يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَرَأَيْتَ إِنْ عَلِمْتُ أَيُّ لَيْلَةٍ لَيْلَةُ الْقَدْرِ مَا أَقُولُ فِيهَا؟ قَالَ : قُولِي : ”اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّي“ رواه الخمسة غير أبي داود، وصححه الترمذي والحاكم.

_An kar6o daga Aisha (ra) tace: Na ce ya Manzon Allah! Idan na dace da daren lailatul Qadr me zan fadi a cikinta? Sai ya ce: *(( Ki ce: Allahumma innaka afuwwun tuhibbul afwa fa’fu annee)).
[ Tirmidzy da Hakim sun inganta shi.]

‘Yan uwa! Wannan addu’ar ita za mu yawaita yi a cikin Wadannan kwanaki goma har mu dace da lailatul Qadr in shaa Allah, Addu’a ce da sunnah ta koyar.

Allah ya datar damu da dukkanin alkhairin da ke cikin wannan dare mai albarka Allah ya bamu ikon lizimtar ta.

[Allahumma innaka afuwwun tuhibbul afwa fa’fu anniy].

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *