Shahararriyar jarumar kannywood wacce akafi sani da suna aisha humairah tayi allah wadai dangane da mutanan da suke tsine mata tare dayi mata kazafi akan banbanci ra’ayi na siyasar kano.
Humairah ta wallafa wani takaitaccen bidiyo akan cewa tana neman alfarma a wurin masoyanta na fadin jihar kano akan cewa dasu zabi gwaninta dan takarar gwamnan jihar kano wato Dr. Nasiru Gawuna da mataimakin shi Garo.
Yayin da wasu daga cikin mabanbanta jam’iyya na jihar suke ganin hakan tamkar cin fuska jarumar tayi musu inda suke ta mayar mata da mummunan martani akan furucin da tayi na cewa al’ummar kano dasu zabi dan takarar nasiru gawuna.
Bayan data wallafa videon, ne mutanan suke ta mayar mata da wannan martanin inda itama ta kara wallafa videon akan masu zaginta cewa wallahi tallahi bazata yafe musu ba, kuma sai allah yayi musu sakayya ranar gobe kiyama.
Aisha humaira ta wallafa bidiyon martanin mai kimanin tsawon minti takwas (8) a cikin shafinta na Tictok, akan masu zagin nata muna fatan allah dai yakiyaye gaba allah kuma yasa sugane cewa zagin musulmi ba abune mai kyau ba cewar jarumar ta kannywood.